Wannan Kungiya tamu mai suna Gaskiya Ta Fi Kwabo, ta dauki lokaci cikin wannan Jamhuriyar Siyasa Ta Hudu (1999 zuwa yau 2023) tana mai nazarin, shin wai, cikin kaf ‘yan siyasunmu na arewacin wannan Kasa a yau, wane mutum ne wanda kirjinsa zai iya daukar nauyin kalmar Hussainin Aminu Kano?
Sai muka rika tarar da mutane iri-iri da kaulanin siyasa wanda babu alamun bullewa cikinsa, ko samun sukunin kai wa gaci, musamman ga bangaren rukunin matasanmu da tuni salon siyasarmu ta yau ta jima da kai su kushewa.
- Yadda Na Gano Angona Ya Yi Zina Da Wata A Ranar Daurin Aurenmu –Wata Amarya
- Hanyoyin Da Suka Kamata ECOWAS Ta Bi Wajen Warware Rikicin Nijar
Da yawan mutanen namu na arewa a yau da muke da tunanin azawa hular sawaba da ke bisa kayin Malam Aminu Kano tsawon lokaci a kan hanyarsa ta samawa Malam Talaka ‘yanci, sai ta gaza yi musu daidai. Ba don komai ba, sai domin banbancin tsarkin niyya wajen shiga lamuran siyasa da suke da shi, tsakaninsu da Malam Aminu Kanon. Da damansu a yau, an yi walkiya, an kai ga fahimtar cewa, ba suna yin siyasa ba ne don gyatta mawuyacin hali da akasarin al’umar Kasar ke ciki.
Babban abin takaicin shi ne, akasarin manyan namu bayan karkare gwajin da muka yi musu bisa sikelin tarihi tare da la’akari da wasu damarmaki da suka samu na shugabanci a rayuwa, sai ta tabbata cewa, kadai dai suna yin siyasa ne don abinda za su samu ne, su je su toshe, duk juyin Duniya, daga su fa, sai dai iyalansu.
Sai akasarin manyan namu suka koma kacokan bisa karuwancin siyasar, ko dai a samu kudi ne, ko kuma a samu wani gwaggwaban mukami. Da kyar da jibin goshi ne muka kai ga gane cewa, muddin idan za a yi batu na gaskiya da adalci ne, Engr. Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ne dan siyasar da a yau cikin arewacin wannan Kasa, za ka yi masa kallon halifar Malam Aminu Kano, kuma Hussaininsa, duba da wasu halaiya na nagarta da ya nuna karara a zahiri, lokacin da yake bisa kujerar gwamnan Kano, musamman daga Shekarun 2015 zuwa 2019.
Ga mutumin da ya yi zamani da Aminu Kano, koko ya yi dogon nazarin lamuran siyasarsa, zai ga a duk motsinsa, maganar Talaka ne cikin kahon zuciyarsa, ta yaya ne talaka zai samu cikakken ‘yanci? Ta yaya ne talaka zai fita daga kangin bauta? Ta yaya ne talaka zai zama wani mutum cikakke mai ra’ayin kansa da makamantansu?. Saboda haka, gatan da Kwankwaso ya ta samma yi wa talaka lokacin mulkinsa, na iya zama wani mizanin da zai tsarkake wannan zabi da kungiyarmu tai masa a matsayin Hussainin na Malam!
Ga yadda abubuwa ke mirginawa a yau cikin wannan kasa, mutum na iya gamsuwa da cewa, la-budda, an dauko wata hanya ne ta kange dan talaka ga samun ilmi mai zurfi musamman a manyan makarantu irin jami’a, duba da irin mamakon kudade da aka kakabawa dalibai cewa sai sun biya. Babu shakka, da Malam Aminu Kano na nan, sai ya yaki irin wannan mummunar ta’adar da ta samo asali daga kundin ‘yan jari hujja. Saboda haka, shi ma Kwankwaso, ya yi duk mai yiwuwa ne, wajen ganin wannan karatu a yau da ake kafulle da shi a gida da waje bai gagari dan Malam Manu ba.
Lokacin da Kwankwaso yake gwamna a Kano ne ya samar da jami’o’i biyu rigis, tare da yunkurin sahale yin karatu cikinsu hatta ga mutumin da bai da ko sisi, muddin dai shi dan Kano ne. Jami’o’in Wudil da Nozwes ne Kwankwaso ya samar, tare da danka amanar tafiyar da su a hannun wasu tatattun masana masu farin tarihi a rayuwa. Bai tsaya kawai ga samar da wadannan manyan makarantu biyu ba, a’a, sai aka ga gwamna Kwankwaso ya fito da wani tsari na fitar da dubban ‘ya’yan talakawa masu hazaka zuwa ga manyan jami’o’in dake a daukacin sassan lardunan Duniya, don karo karatu. Don su je su karo zuzzurfan karatun da zai kai su har ga matakin karatun digirin digirgir. Mutane marasa galihu, wadanda tun da Allah Ya halicce su, ba su ma taba zuwa ko da filin jirgi ne ba, amma cikin taimakon Allah sai ga su a filin jirgi, za ma su fita kasashen ketare yin karatu ne. Zancen nan da ake yanzu, wasunsu sun zama Daktoci, wasunsu ma Farfesoshi ne.
Hussainin na Aminu Kano, Kwankwaso, bai tsaya ne ba kawai ga jami’o’in ketare da kuma jami’o’i guda biyu da ya samar cikin Kano, sai kuma ya tashi haikan wajen cike duk wani gurbin karatu na mutanen Kano da ke cikin wasu jami’o’in sassan wannan Kasa, yana tura daliban daga jihar Kano zuwa can, tare kuma da biya musu duk wasu kudaden makaranta da ake da bukata.
Duk da irin wancan gata salo bayan salo da aka lasafto, da Kwankwaso ke yi wa dan talaka a wancan lokaci a fannin na ilmi, sai kuma ya kara kirkiro wani kwamiti da ya kira shi da CRC “Community Re-orientation Council” wanda shi ma da yawan aikace-aikacen kwamitin na da jibi da harkar ilmi ta bangarori da dama. Sai ya zamana cewa, wannan kwamiti na dinka dubban yadina tare da rabar da su ga daliban makarantun firamare na daukacin jihar Kano kyauta. Sai kuma aka sake fito da wani sabon tsarin ciyar da daukacin daliban na jihar Kano, shi ma kyauta. Saboda ingancin wannan tsari na ciyarwa, hatta tsohuwar gwamnatin taraiya karkashin Buhari, ta kwaikwaya tare da dabbakawa. Litafai ma kyauta ne aka rika rabarwa ga daukacin yara da ke karatu a makarantunmu na firamaren Kano. Ga gina sabbin makarantun sakandire da na firamare, tare da yin kwaskwarima da sauran gyare-gyare a makarantun. Hakika Hussainin Aminu Kano Kwankwaso, ba karamin tagomashi ne yai wa harkar ilmi a Kano ba, kafin daga bisani gwamnatin da ta gaje shi ta ragargaza tare da tarwatsa duk wasu kyawawan tanade-tanade da aka yi wa bangaren na ilmi a lokacin Daular Kwankwasiyya.
Koyar da sana’o’i ga matasa tare da ba su jari, wani lamari ne da gwamnatin Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ba ta dauke shi da wasa ba. Sannan, wadanda ke da sana’o’in babu jari, suma gwamnatin ta Madugun Kwankwasiyya ba ta sa su a mala ba, don kuwa an dube su da idon rahama, ta hanyar sahale musu samun bashi daga kananan bankunan Makrofainans “Microfinance Banks”. Irin wadannan bankunan ba da lamunin rance ga masu karamin karfi ko kananan sana’o’i, sai da Kwankwaso ya samar da akalla guda talatin da bakwai (37) a fadin jihar ta Kano.
Sai da Kwankwaso ya samar da wuraren koyawa matasa sana’o’i guda ashirin da biyu (22) a fadin jihar. Bugu da kari, sai kuma gwamnatin ta Kwankwaso ta samar da wani tsari da ta kira shi da “Lafiya Jari”. Karkashin shirin, a na bayar da mamakon jari ne ga kunzumin matasa, na su je su kama shago, su biya haya, su sayo magunguna su zuba don sayarwa. Da daman matasa a wancan lokaci, tattalin arzikinsu ya bunkasa, sun mallaki tarin kadarori a sanadiyyar wannan shiri na Lafiya Jari.
Babu shakka, sabanin irin yadda akasarin manyan ‘yan siyasarmu na arewa ke rikon matasa a matsayin wata kariya a gare su yayin fita yawon kamfen, ba haka lamarin yake ba tattare da Hussainin Malam Aminu Kano, Kwankwaso. Hatta irin wadancan matasa ‘yan daba ko a ce ‘yan jagaliya, daular Kwankwasiyya ba ta yashe su ba, ta ma ja su ne a jiki, tare da sama musu wata mafita a rayuwa, ta hanyar bude musu wani dakin shan magani a kauyen Jido, da ke a garin Wudil, inda ake ba su wata kulawa ta musamman, don kashe kaifin tasirin irin wadancan muggan kwayoyi da suke sha.
Samar da hukumar KAROTA da hukumar KARMA da Engr Dr Rabi’u Kwankwaso ya yi, duka sun fi gaban a mance da irin gudunmuwar da har kawo wannan lokaci suke bayarwa ga daukacin jama’ar Kano.
Samar da asibitoci dari shida (600), wadanda ko dai an gina su ne, koko an gyara su ne, na nan cikin kundin tarihin Kano da na Kwankwasiyya. Samar da kwararrun likitoci kusan dari uku (300) a fage na kwarewa iri-iri da Madugun na Kwankwasiyya ya samar a Kano, babu shakka abin a yaba ne.
A fili yake ga mai neman gaskiyar lamari, a yau cikin ‘yan siyasar Arewacin Nijeriya, ba ka da wani halifan Malam Aminu Kano sama da Rabi’u Musa Kwankwaso. Ban da shi a yau, wane dan siyasa ne da ba ya ba da kudin mota da na kashewa yayin tararsa, amma sama dan’adam dubu dari biyar ke tarbarsa cikin shauki da annashuwa?.
Wane dan siyasa ne ke rangada gwamnatin jiha da ta taraiya a lokaci guda a zabe?. Wane dan siyasa ne da akasarin talakawan Kasa ke shaukin ya zamto shugaban Kasa sama da shi?. Akwai misalai iri-iri da mutum ka iya bijirarwa nan take, da ke nuna wajibcin sallamawa Kwankwaso matsayin Halifa kuma Hussainin marigayi Malam Aminu Kano.