• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aikatar Wajen Kasar Sin Ta Musanta Kalaman Amurka Da Birtaniya Game Da Yankin Hong Kong

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

Wasu rahotanni na cewa, Amurka da Birtaniya, da dai sauran wasu kasashen yamma, sun fitar da sanarwar da ma kalamai mabambanta, a dab da ranar bikin murnar cikar yankin Hong Kong shekaru 25 da komawa karkashin ikon kasar Sin.

Cikin irin wadancan kalamai dai, kasashen na yamma sun rika cewa, wai an lalata dimokaradiyya da tsarin bin doka, da ‘yancin al’umma a Hong Kong. Kaza lika wai a cewar su, kasar Sin ta gaza cika alkawarin ta na aiwatar da manufar nan ta “Kasa daya amma tsarin mulki biyu “.

  • Ko Kun San Dakin Ibadar Aljannar Duniya Na Kasar Sin?

Game da wadannan zarge zarge, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce wadannan kasashe ba su cancanci furta kalaman batanci kan Hong Kong mai bunkasuwa da daidaito ba.

Zhao Lijian, wanda ya yi wannan tsokaci a yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya kara da cewa, shugaban kasar Sin ya gabatar da muhimmin jawabi, a bikin cikar yankin Hong Kong shekaru 25 da komawa karkashin kasar Sin, ya kuma jaddada manyan nasarorin da aka cimma, a fannin aiwatar da manufar nan ta “Kasa daya amma tsarin mulki biyu ” cikin shekarun 25 da suka gabata, kuma ya yi nuni da cewa, a bayyane take, manufar “Kasa daya amma tsarin mulki biyu” tana da inganci, an kuma gwada nagartar hakan a zahiri, manufar ta kuma dace da babbar moriyar kasar Sin baki daya, da moriyar yankunan Hong Kong da Macao, ta kuma samu cikakken goyon bayan sama da al’ummar Sinawa biliyan 1.4, da al’ummun dake zaune a yankunan HK da Macao, baya ga amincewa da ta samu daga sassan kasa da kasa. Har ila yau, gwamnatin tsakiyar kasar Sin, za ta ci gaba da aiwatar da manufar “Kasa daya amma tsarin mulki biyu” cikin tsawon lokaci, kuma ba za ta taba sauya matsayar ta a kan hakan ba. (Saminu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
Daga Birnin Sin

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

October 11, 2025
Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
Daga Birnin Sin

Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

October 11, 2025
An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

October 11, 2025
Next Post
NIS Reshen Bayelsa Ta Horas Da Jami’anta A Kan Kyautata Rayuwarsu

NIS Reshen Bayelsa Ta Horas Da Jami'anta A Kan Kyautata Rayuwarsu

LABARAI MASU NASABA

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025

October 11, 2025
Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

Tarihin Hassan Usman Katsina (1)

October 11, 2025
An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique

October 11, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari

October 11, 2025
Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia

Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia

October 11, 2025
Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa

Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

October 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.