Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta ce ta kadu da jin yunkurin sojoji masu juyin mulki a Nijar na tuhumar zababben shugaban kasa Bazoum Mohamed da zargin babbar cin amanar kasa.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar sa’o’i bayan kalaman sojojin na yi wa Bazoum shari’a, ECOWAS ta ce matakin wani takalar fada ne daga shugabannin sojin.
- NIS Ta Yi Gargadi Kan Ma Su Balaguro Ta Haramtacciyar Hanya
- Kwamitin Majalisa Ya Himmatu Wajen Kammala Hanyar Abuja- Kaduna Zuwa Kano
Ta kuma ce hakan ya ci karo da rahotannin da ake yadawa cewa sabbin masu mulkin Nijar din sun nuna sha’awar bin hanyar masalaha don kawo karshen dambarwar da ake ciki.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hambararren shugaban ksar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar kasa.
Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen kasar, zagon kasa.
Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne, ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta kasar.
Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani daki na karkashin kasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hambarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.
Baya ga shugaban sojojin sun kuma kama wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatinsa da ma na jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya.
Mai magana da yawun gwamnatin sojin ya ce tuni sun riga ma sun tattara duk wasu bayanai da shaidun da suke bukata domin gurfanar da Bazoum a gaban shari’a.
A sanarwar, kakakin ya ce, za su gurfanar da Bazoum tare da wadanda ya kira masu hada baki da shi a cikin kasar da ma ketare a kan laifukan da suka zayyana, saboda musayar bayanan da ya yi tsakaninsa da wasu ‘yan kasashen waje da shugabannin kasashe da kuma shugabannin kungiyoyin kasashen duniya.
Bayan karbe mulki tare da rushe zababbiyar gwamnatin tuni suka nada majalisar ministoci, tare da yin biris da duk wani kira na neman sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya, daga ECOWAS da sauran kasashe da hukumomi masu rajin kare dimokradiyya na duniya.