Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, farashin man fetur ba zai karu ba.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), Cif Chinedu Ukadike, akwanakin baya ya bayyana cewa, akwai yiwuwar kara farashin man fetur nan gaba kadan duba da yadda darajar Naira akan dalar Amurka ke ta faduwa a kasuwa.
Ukadike ya bayyana cewa, “Yanzu dalar Amurka daya tana kaiwa Naira N910 zuwa N940, kuma ta kusa kaiwa N1,000. Don haka, ‘yan Nijeriya su shirya siyan litar man fetur daya akan Naira N750.
Amma da yake magana ta bakin Ajuri Ngeale, mai magana da yawunsa, Tinubu ya shaidawa ‘yan Nijeriya cewa ba za a samu wani kari ba a yanzu.