Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan kasashe musamman wadanda ba su nuna adawa da juyin mulkin da suka yi ba a kasar ba.
A ranar Talata firaministan Nijar da sojoji suka nada, Ali Mahaman Lamine Zeine, tare da wasu mambobin majalisar mulkin soja biyu suka ziyarci Chadi domin tattaunawa da shugaban kasar, Janar Mahamat Idriss Deby.
- Kotu Ta Dakatar Da Sanata Ali Ndume Kan Yi Wa Wani Malami A Abuja Karan Tsaye
- Manchester City Ta Lashe Kofin Super Cup Bayan Lallasa Sevilla
Zeine, wanda ya je a matsayin fuskar diflomasiyya ta gwamnatin soja – ya ce a yanzu kasarsa na karkashin gwamnatin mulkin soji, yana mai cewa a shirye suke da su bude kofar tattaunawa.
Kazalika, sojojin mulkin sun tura wata tawaga zuwa Guinea ranar Asabar da ta gabata, duka dai da zimmar neman goyon baya.
Kafin haka, sabon ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody, ya je Mali a ranar Juma’a cikin wata gajeriyar ziyara.
Ƙasashen Mali da Burkina Faso da Gueinea mambobin ECOWAS ne – kungiyar da ke raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma – amma ta dakatar da su sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen.
Haka nan dukkansu sun ci alwashin goya wa Nijar baya idan dakarun ECOWAS ko na wata kasar waje suka kai wa sojojin hari.
A karshen makon da ya gabata gwamnatin sojin Mali ta sanar cewa za ta aika wa Nijar nau’in kayan abinci na hatsi kamar dawa masara da gero saboda takunkumin ECOWAS da ya hana sayar mata da kayayyaki.
Chadi ba ta cikin kungiyar ECOWAS, sannan kuma ba ta nuna adawa karara da juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi ba, amma ta bayyana a fili cewa ba za ta goyi bayan yin amfani da karfi a kan makwabciyar tata ba.
Har yanzu ECOWAS na ci gaba da yunkurin difilomasiyya don sasanta rikicin siyasar, duk da barazanar amfani da karfin soja don taka wa sojojin karkashin Janar Abdourahmane Tchiani birki.
A ranar Alhamis da Juma’a hafsoshin tsaron kungiyar za su yi taro a birnin Accra na Ghana don ci gaba da tattaunawa bayan shugabannin Ecowas din sun ba su umarnin É—aura damarar kutsawa Nijar a makon da ya gabata.
A gefe guda kuma, fitattun mutane da kungiyoyi a Nijeriya na ci gaba da nuna adawa da yin amfani da karfin yayin da Shugaba Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ECOWAS, yake jagorantar yunkurin.