Gwamna Babagana Zulum na Borno ya amince da fitar da Naira miliyan 308 don biyan tallafin karatu ga dalibai marasa masu karamin karfi su 14,416 da ke jihar.
Babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Malam Bala Isa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a.
- Tsadar Rayuwa: Gwamna Zulum Ya Raba Wa Magidanta 2000 Kayan Abinci
- Zulum Ya Cire Sunan Ngoshe Daga Sunayen Kwamishinonin Borno
Biyan kudaden zai saukaka biyan kudin makaranta ga dalibai na shekarar karatu na 2021/2022.
Biyan tallafin zai baiwa hukumar damar kammala biyan kudaden karatu na shekarar 2021/2022, inda ya kara da cewa, “yanzu za mu mayar da hankali kan shekarar karatu na 2022/2023.
“Gov. Babagana Zulum ya lura cewa a halin yanzu dalibai na ci gaba da gudanar da harkokin ilimi a daidai lokacin da iyaye ke fuskantar kalubalen tattalin arziki ga bukatun dalibai.
“Amincewar biyan zai taimaka matuka wajen sauke nauyin da daliban ke da shi na ilimi a kan iyayensu.
“Gwamnan ya kuma bukaci daliban da su kasance masu jajircewa da mayar da hankali kan karatunsu, tare da yin amfani da tallafin da suke samu yadda ya kamata domin ci gaban ilimi”.
Da yake tsokaci, Ahmad Kyari, jami’in kungiyar daliban jihar Borno (NUBOSS), ya yaba da wannan matakin, yana mai bayyana hakan a matsayin abun da ya dace”.
Kyari ya ba da tabbacin yin amfani da taffin yadda ya dace.