Janar Tchiani ya ce nan da wata daya za su kafa kwamitin da zai yi nazari kan sabon kundin tsarin mulki na kasar.
Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya ce za su mika mulki ga gwamnatin farar-hula nan da shekaru uku masu zuwa.
- Zantawa Da Dilma Rousseff, Shugabar Sabon Bankin Samar Da Ci Gaba
- Kwamandojin Boko Haram 4 Da Wasu 13 Sun Mika Wuya Ga MNJTF
Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin na kasar ranar Asabar da daddare.
Ya yi jawabin ne jim kadan bayan ya gana da tawagar kungiyar ECOWAS, karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar.
Janar Tchiani ya ce nan da wata daya za su kafa kwamitin da zai yi nazari kan sabon kundin tsarin mulki na kasar.
Ya kara da cewa Nijar ba ta son zuwa yaki kuma kofarsu a bude take su tattauna, amma kuma za su kare kansu idan bukatar hakan ta taso.
A gefe guda, tawagar Kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar ta gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum a Yamai, babban birnin kasar ranar Asabar.
Tawagar ta je Yamai ne domin lalubo hanyar magance rikicin siyasar da kasar ta fada a ciki tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.
Janar Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa tawagarsa ta saurari bayani daga wurin Bazoum da kuma kalubalen da yake fuskanta tun da aka kifar da gwamnatinsa.
“Mun gan shi mun ji nashi ra’ayin da abin da aka yi mashi. Kuma akwai wasu ‘yan matsaloli wadanda ke tare da shi da ya yi mana bayani wadanda za mu gaya wa shugabanninmu,” in ji shi.
Ko da yake bai yi karin bayani game da ganawar ba, amma ya ce “wannan taro da aka yi Allah ya sa an samu mabudi ke nan da za mu ci gaba da tattaunawa don a samu a warware wannan matsala.”
Tun da fari Firaiministan kasar Ali Mahamane Laminé Zeine ya tarbi tawagar a filin jirgin sama na Diori Hamani.
Wannan tattaunawar na zuwa ne kwana guda bayan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS sun kammala taronsu a Ghana inda suka saka ranar da za su tura dakarunsu Jamhuriyyar Nijar idan hanyoyin diflomasiyya suka ci tura.
Wannan ne karo na biyu da wakilan ECOWAS karkashin jagorancin Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ke zuwa Nijar domin sulhu.
A karon farko ba su samu ganawa da Janar Abdourahamane Tchiani ba inda suka koma ba tare da an cimma wata matsaya ba.
A ranar Juma’a ne kasashen Mali da Burkina Faso suka aike da jiragen yaki Nijar domin tallafa wa sojojin kasar kan duk wata barazana da za su fuskanta daga dakarun ECOWAS.