Mai magana yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, Sin ta bayyana rashin jin dadinta ga kasashen da abin ya shafa dangane da kokarin shugabannin kasashen Amurka da Japan da Koriya ta Kudu na neman bata suna da takalar kasar Sin da suka yi a yayin ganawarsu a Camp David.
Wang Wenbin ya shaidawa taron manema labarai na yau da kullum Litinin din nan cewa, shugabannin kasashen uku sun shafawa kasar Sin bakin fenti da ma takalar kasar kan batutuwan Taiwan da tekun kudancin kasar Sin a gun taron na Camp David, da yin katsalandan ga harkokin cikin gidan kasar Sin, da neman tayar da zaune tsaye tsakanin Sin da kasashen dake makwabtaka da ita, wanda hakan ya keta muhimman ka’idojin raya dangantakar kasa da kasa matuka. (Ibrahim)