Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Malam Uba Sani, ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta shirya tsaf don fara raba tallafi ga marasa karfi a jihar wadanda cire tallafin fetur ya jefa cikin mawuyacin hali.
Gwamnatin jihar ta tattauna da shugabannin al’umma game da abun da ya fi cancanta gwamnatin ta yi akan Naira Biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta fara bayarwa don tallafawa al’umma.
Kwamitin gwamnatin karkashin jagorancin Mataimakiyar gwamnan, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ne ya tattauna da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu, wakilan ‘yan kasuwa, wakilan ma’aikatan gwamnati, kungiyoyin Manoma da Malamai da sauransu.
A sakamakon tattaunawar, kwamitocin sun cimma matsaya kan yadda za a kashe kudin, inda suka raba aikin zuwa gida Uku, kamar haka:
Na farko, za a siya buhunan shinkafa guda 40,000 wanda za a tabbatar mutum miliyan 1,050,000 marasa karfi sun amfana da wannan tallafin. Daga cikin biliyan biyun, za a kashe Naira biliyan N1,935,000,000 sannan ragowar Naira Miliyan N65,000,000 za a yi amfani da su wurin tallafawa marasa karfi don zuwa wurin da za a raba abincin.
Na biyu, za a hada kai da kungiyoyin sufuri kan rage kudin mota don taimakawa mutane wurin zirga-zirgarsu ta yau da kullum. Bayan wannan kuma, gwamnatin za ta siyo motocin sufuri na jihar Kaduna wanda za a rage kudinsu wasu kuma za a barsu shiga kyauta. Bugu da kari, gwamnatin za ta tabbatar ta samar da takin zamani don taimakawa manoma don bunkasa harkar Noma a jihar
Na Karshe, Gwamnan ya bayyana cewa, tuni ya fara tattauna da Sakataren Dindindin na ma’aikatar sufuri kuma zai gana da sabon Ministan sufuri kan yadda za a dawo da layin dogo da ke zirga-zirga acikin jihar wanda ke ta so wa daga Zaria zuwa cikin Kaduna sannan ya nufi Kafanchan.
Gwamnan ya kuma bukaci jama’a da su kara hakuri, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar Kaduna wurin nemo mafita don inganta harkoki da rayuwar ‘yan jihar.