Akalla ‘yan bindiga takwas ne suka rasa rayukansu acikin kwanaki biyun da suka gabata a wasu kauyuka biyu na Chitto da Gbeji, da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwe.
Daily Sun ta tattaro cewa, ‘yan ta’addar sun kashe kansu ne yayin da tawagoginsu biyu da ke gaba da juna suka gamu inda suka fara artabu. An kuma tattaro cewa ‘yan bindigar, sun kuma kona wata kasuwa a yankin.
Mazauna yankin, wadanda suka so a sakaya sunansu, sun ce an kashe mutane biyar a kauyen Chitto ranar Litinin, yayin da wasu uku kuma aka kashe su a kauyen Gbeji a ranar Talata. Mazauna yankin, sun bayyana cewa har yanzun tawagogin ‘yan ta’addar biyu na ci gaba da yakar juna har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto, a jiya Talata.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, dan majalisar dokokin jihar Benuee mai wakiltar mazabar Ukum, Engr. Ezra Nyiyongo, ya tabbatar da rahoton, inda ya ce jami’an tsaro a yankin sun ce kawo yanzu an gano gawarwaki uku.