Ana zargin gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda da yin rufa-rufa a kan kudaden da aka kashe wajen sayen masara domin raba wa al’umma.
Rahotanni sun ce gwamna Dikko Umar Radda ne ya bada umarnin sayen masara buhu 36,100 domin raba wa a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina da niyyar rage radadin rayuwa da ake fama da shi.
- Rushewar Gini: Wike Ya Umarci A Cafko Mamallakin Ginin Cikin Gaggawa
- Dan Bindiga Ya Harbe Mutum Da Raunata Wasu Da Dama A Amurka
To sai dai batun da ya dabaibaye wannan shiri na bada tallafi shi ne, yadda gwamnati tun daga gwamna zuwa Kwamishinoni da shuwagabannin Kananan hukumomi suka yi gum wajen kin bayyana ko nawa aka ware domin yin wannan hidima.
Yanzu haka yatsan zargi na nuna cewa akwai wani abu da ake boyewa a kan wannan shiri na raban kayan abinci wanda wasu mutane suka ce tiya daya ta masara suka samu wasu kuma suke ce sun samu gwangwanin shinkafa uku duk da sunan tallafi.
Shugaban karamar hukumar Kaita kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi, injiniya Bello Yandaki ya bayyana cewa wannan tallafi hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Katsina da kuma kananan hukumomi inda kowane bangare zai bada kashi 50.
Wannan yunkuri da gwamnati ta yi da yawa jama’a sun kalle shi ta fuskar taimako da rage radadin mawuyacin halin da aka shiga wannan gwamnati ga Bola Ahmad Tinubu.
Dangane da batun ko nawa aka ware domin sayo wadanda kayayyaki ya bayyana cewa shi dai na karamar hukumar sa kawai ya sani bai san na saura ba.
Ganin yadda shugaban kungiyar shuwagabannin Kananan hukumomi ya ja daga cewa baya da ikon bayyana ko nawa aka kashe yasa yatsan zargi ke nuna gwamnatin Dikko Radda da yin rufa-rufa da kudaden ƙananan hukumomi wanda ya ce zai sakar masu mara su yi fitsari idan ya zama gwamna.
Wani abu da ke ba jama’a mamaki a kan wannan lamari shi ne yadda manyan jami’an gwamnatin jihar Katsina suka yi gum da bakinsu wajan bayyanawa duniya makudan Kudaden da aka kashe wajen bada wannan tallafi da wasu suka samu tiyar masara daya wasu kuma suka kare da gwangwanin shinkafa uku.
Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu na jihar Katsina Farfesa Badamasi Charanci na daga cikin jami’an gwamnati da ya kamata su maganta amma yaki yarda ya hadu da ‘yan jarida domin tattaunawa a kan wannan batu.
Shima kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai Hon. Bala Zango ya shafawa idanunsa toka inda ya bayyana cewa Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu ne ke da alhakin yin wannan bayani ba shi ba.
Wani dalili da ke saya ana yi wa gwamnatin jihar Katsina kallon hadarin kaji game da kin bayyana ko nawa ta kashe wajan sayen masara da aka raba a Kananan hukumomi shi ne, yadda gwamnati ta bayyana karbar Naira biliyan 2 sannan ta bada umarnin a sayi shinkafa buhu 40,000 da kudin baki daya.
Yanzu haka jama’a da dama na kallon wannan abu tamkar wata rufa-rufa ce da kudaden jama’a da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta yi rantsuwa cewa za ta kula da su kuma ta yi amfani da su yadda ya kamata.
To sai dai ko me ya sa suke tsoron bayyanawa duniya cewa ga adadin kudaden da aka kashe domin sayen masara buhu dubu 36,100 wanda aka raba shi ga kowace mazaba buhu 100.