Akalla mata 48 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su ne suka samu ‘yancin walwala a kauyukan Maiwa da Shuwarin da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno.Â
Kwararren mai sharhin lamuran tsaro a yankin Lake Chad, Zagazola Makama, shi ne ya sanar da wannan matakin a ranar Alhamis, inda ya ce matan sun tsira daga inda ake tsare da su ne a ranar Laraba.
- BRICS Na Taka Rawar Gani Ga Ci Gaban Nahiyar Afirka
- Badaru Na Da Kwarewar Jagorantar Ma’aikatar Tsaro – ANA
Makama ya tabbatar da kubutar matan ne a shafinsa na X da aka fi sani da Tiwuta, ya kara da cewa, ‘yan Boko Haram din sun yi garkuwa da matan ne a ranar 22 ga watan Agustan 2023 a lokacin da suke gonakansu.
A cewar Makama, an kwashi matan ne zuwa wani wajen da ba a sani ba, kuma bayan garkuwa da su din ‘yan Boko Haram sun nemi fansar kudade daga hannun iyalansu.
“A ranar Laraba ne aka saki matan bayan biyan kudin fansa na naira N50, 000 ga kowannensu da aka bai wa ‘yan ta’addan,” Masanin ya shaida.
Makama ya kuma ce akwai wasu mata su 8 da tun da farko aka sake su bayan sun biya naira 20,000 ga kowannensu.