Yau Lahadi 27 ga watan nan ne kakakin ofishin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin dake Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin, ya soki, tare da bayyana adawa da sanarwar da majalissar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar, wadda a ciki ta zargi matakin wajibi da hukumar ‘yan sandan HK ta dauka, domin kiyaye tsaron yankin, kana ta tsoma baki a cikin harkokin HK da harkokin kasar Sin.
Kakakin ya bayyana cewa, tun bayan da aka aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong, an tabbatar da kiyaye hakkoki daban daban na mazauna yankin bisa doka yadda ya kamata, kuma babu wata kasa wadda ke iya yin biris da matakan lahanta tsaro, don haka ya zama wajibi a dauki mataki domin kiyaye tsaron kai.
Jami’in ya ce kasancewar a yanzu haka akwai wasu mutane dake kokarin tayar da tashin hankali a Hong Kong, da nufin kawo baraka ga kasar Sin, ya sa ‘yan sandan yankin suka dauki mataki na wajibi bisa doka, don haka bai dace a zargi matakin da suka dauka ba.
Kakakin ya yi nuni da cewa, Amurka ita ma tana kiyaye tsaron kasarta bisa doka, kuma ta kan sanya takunkumi kan sauran kasashe ba bisa ka’ida ba, don haka ya dace Amurka ta yi la’akari da yanayin da take ciki, bai kamata ta soki matakan tabbatar da tsaron kasa da aka dauka a HK bisa doka, bisa ra’ayin kashin kan ta ba. (Mai fassara: Jamila)