Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya na dandana kula luransu a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Litinin da ta gabata, cewa babbar jam’iyyar adawar ta koka kan yadda Nijeriya ta shiga tsaka mai wuya a karkashin jam’iyyar APC da Tinubu yake jagoranta, wadda ba ta damu da ‘yan kasa ba, al’amarin da ya haifar da yanayi na rashin nagartaccen shugabanci a kasar nan.
- Ba Za Mu Sake Lamuntar Kumbiya-kumbiyar Da Ake Tafkawa Wurin Fasfo Ba – Ministan Cikin Gida
- Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Tallafawa Mali Bayan Janyewar Dakarun MINUSMA
Sanarwar ta kara da cewa, “Jam’iyyar ta firgita da yadda aka samu rashin jituwa mai tsanani tsakanin gwamnati da ‘yan kasa sakamakon rashin tsari da kuma gaggawar aiwatar da manufofin da suka kawo wahalhalu mai tsanani, rashin tsaro da kuma fargabar da tuni ke barazana ga zaman lafiyar al’umma da hadin kai da wanzuwar kasar nan.
“Rashin wayo ne da sanin ya kamata da gwamnati ta yi wajen cire tallafin man fetur da karya darajar naira wanda ya janyo tsadar rayuwa da ya gurgunta mana tattalin arzikin kasa, sannan ya durkusar da miliyoyin ‘yan kasuwa tare da jawo asarar ayyuka masu dimbin yawa da karuwar talauci da yunwa da rashin tsaro a fadin kasar nan.
“Lmarin ya janyo mummunar asarar ga masu saka hannun jari tare da ficewar kamfanonin tare da barin miliyoyin ‘yan Nijeriya neman aikin yi da gurgunta masu kanana da matsakaitan masana’antu wadanda su ne ainihin ginshikan tattalin arzikin kasarmu.
“Abin ban tsoro ne cewa a cikin watanni biyun da suka gabata, sama da ‘yan Nijeriya miliyan 150 ba za su iya ciyar da iyalansu abinci ba, inda suke kwana da yauwa.
“Abin takaici ne yadda gwamnatin APC ke ci gaba da yaudarar ‘yan Nijeriya da bayar da tallafi na raba buhunan shinkafa 1,200 ga mutane a kowace jiha. Jam’iyyar APC ta fadada karfinta na yaudara da damfarar ‘yan Nijeriya ta hanyar shirye-shiryen marasa amfani.”
PDP ta bayyana damuwata game da abin da ta lura akwai rashin tausayi, damuwa da raba kan ‘yan kasa, idan ba a yi gaggawar magance lamarin ba zai iya harfar da mummunan rikici.”
Ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu su kasance masu bin doka da oda da kuma mara wa juna baya a kokarinsu na samar da kasa mai tsaro da ci gaban tattalin arziki.