A ranar Asabar ne Hukumar Raya Birnin Abuja ta fara rusheirushen shagunan kanikawa da suke harkokinsu ba bisa ka’ida ba a kan babar hanyar Nyanya, musamman a wuraren da ake ware don kasuwan dabbobi ta Kugbo a kan hanyar Abuja-Nyanya zuwa Keffi.
Mataimaki na musamman ga MInistan Abuja, Mista Ikharo Attah, ya jagoranci aikin rusau din ya kuma ce fiye da shekara 3 kenan aka basu takardar wa’adi na rusau din da kuma umarar su tashi daga inda suke harkokinsu na kanikanci.
- An Umarci Sarakunan Gargajiya A Katsina Da Su Tabbatar Da Jama’arsu Sun Yi Rajistar Zabe
- Wata Kungiya Ta Bukaci Zaurawa Da Su Rungumi Sana’o’in Dogaro Da Kai
Ya kuma kara da cewa, a baya-bayan nan wata 5 da suka wuce an sake basu takardrar wa’adin tashi amma suka yi biris.
Ya kuma bayana cewa, aikin rusau din ya zama dole ne don masu wurin sun yi ta kai korafi na bukatar wurinsu don su cigaba da gudanar da harkokinsu.
A kan haka ya bukaci kanikawa su tafi inda aka ware musu don gudanar da harkokinsu.