Akwai abubuwan da suka ja hankali a lokacin yanke hukunci a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, wanda ya gudana a Abuja a wannan makon da muke ciki.
Kotun sauraron kararrakin zaben na shugaban kasa, ta yi watsi da galibin korafe-korafen da aka shigar a karar da Mista Peter Obi na jam’iyyar LP da Atiku Abubakar na PDP suka shigar a kan kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun 2023.
- Zabe: Obi Ya Gaza Bayyana Yadda Ya Samu Kuri’u Masu Rinjaye – Kotun Zaben Shugaban Ƙasa
- Daraktoci Da Jami’an FCT 7 Na Fuskantar Tuhume-tuhume Kan Badakar Fili
Mai shari’a Haruna Tsammani, wanda ya jagoranci kwamitin Alkalan guda 5 na kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ya yi watsi da karar sakamakon rashin nagarta, inda ya kara da cewa masu shigar da kara sun kasa tabbatar da zargin da suka yi kan zaben.
Obi da jam’iyyarsa a cikin karar da suka shigar a watan Maris na wannan shekara, sun yi ikirarin cewa Tinubu bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
Bugu da kari, sun yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ba ta bi ka’idar da doka ta shimfida ba wajen ayyana Tinubun a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Bayan haka, Obi da LP sun yi ikirarin cewa bai kamata Tinubu ya kasance a zaben ba, saboda hanyar da ya bi wajen zaben mataimakinsa ba bisa ka’ida ba da kuma zarge-zargen da wata kotu a Amurka ta yi masa a shekarar 1990.
Masu shigar da karar, sun zargi INEC da ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da bai samu kashi 25 na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya (Abuja) ba.
Sai dai da yake yanke hukunci a cikin karar ranar Larabar da ta gabata, Mai Shari’a Tsammani ya ce wadanda suka shigar da karar sun kasa tabbatar da zarge-zargen da suke yi na tafka magudi, rashin bin ka’ida da kuma ayyukan rashawa da aka yi a zaben.
A kan batun rashin samun kashi 25 da Tinubu ya gaza samu a cikin Babban Birnin Tarayya, kotun ta ce Abuja daidai take da kowace jiha a Nijeriya.
Kotun ta yi nuni da cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya bayyana cewa dukkanin ‘yan kasa daidai suke, babu wanda ya fi wani ko kasa da wani ta hanyar zabe.
Tsammani ya yi nuni da cewa, masu shigar da kara sun yi fassarar sashe na 134 na kundin tsarin mulkin kasar, ba daidai ba, inda suka dauka cewa masu kada kuri’a na Abuja sun fi kima ga wasu jihohi.
Kotun ta ce sashe na 299 na kundin tsarin mulkin kasar, ya ce, “ Abuja kamar kowace jiha take” kuma ba ta fi sauran jihohi ba.
Tsammani ya kara da cewa, “Bayan an warware dukkanin batutuwan guda uku don goyon bayan wadanda ake kara, shari’ar wadanda suka shigar da kara ta kasance mara tushe da kuma nagarta.”
Sai dai kuma jam’iyyar LP ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar da ta tabbatar da Bola Tinubu na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga Fabrairun, 2023.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Obiora Ifoh, ya bayyana matsayin jam’iyyar a Abuja, jim kadan bayan kotun ta bayyana hukuncin nata.
Ifoh ya ce, “Jam’iyyar LP ta yi watsi da karar da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, karkashin jagorancin mai shari’a Haruna Tsammani ta yi a yau, kuma ba za mu amince da sakamakon hukuncin da aka yanke ba, saboda ba a yi adalci ko kadan ba.
“’Yan Nijeriya shaidu ne kan zaben da aka yi a ranar 25 ga Fabrairun 2023, wanda duniya ta yi Allah wadai da shi amma kotun ta yi watsi da hujjojinmu.”
“Demokuradiyya ake yi kuma ba za mu yi kasa a guiwa ba, har sai mun kai ga yin nasara. Kazalika, muna jinjina wa tawagar kungiyar lauyoyinmu da suka yi namijin kokari a kan wannan shari’a.
Muna ikirarin mulkin dimokuradiyya a Nijeriya ne kawai, amma ba ita ake yi ba, domin haka ba za mu yi kasa a guiwa ba,
Za mu gabatar da cikakkun bayanai game da matsayar jam’iyyarmu, bayan tattaunawa da lauyoyinmu domin cimma matsaya,” in ji shi .
“Haka nan, muna kira ga dukkanin masoya mulkin dimokuradiyya da su mai da hankali da kwarin guiwa domin kawo sauyi a Nijeriya.”
Har ila yau, kotun sauraron karar zaben shugaban kasar ta kori zargin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar kan cewa, Tinubu ba dan kasa ba ne sannan kuma yana ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Yayin da kotun ta yi watsi da karar Atiku kan zargin cewa Tinubu yana amfani da takardar kasashe guda biyu. Haka kuma ta yi fatali da zargi cewa Tinubu bai cancanci ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya ba.
Haka kuma, an hango wasu daga cikin mahalarta kotun sauraron karar zaben shugaban kasar, na ta faman sharbar bacci kafin yanke hukuncin.
Haka nan wani lauya ya yi kokarin gabatar da korafi, sai dai Alkalan kotun sun ki ki amincewa tare da ankarar da shi cewa ya bari idan yana da magana bayan yanke hukunci sai ya yi nazari ya san matakin da zai dauka.
Wannan hukunci ko kadan bai yi wa bangaren Obi da Atiku dadi ba, inda ake ganin cewa ko shakka babu za su garzaya zuwa Kotun Koli.