Ministan Albarkatun Teku, Adegboyega Oyetola, ya bayyana cewa, akwai bukatar a gaggauta farfado tare dda bunkasa kayayyakin aiki da ke tashar jiragen ruwa na Apapa da Tin-Can Island da ke Ledgas, ya kuma yaba da yadda Shugaban Tashoshin Ruwan Nijeriya NPA Muhammed Bello Koko yake gudanar da ayyukansa.
Ministan ya bayyana haka ne a yayin da kai ziyarar gani da ido a tashar jiragen ruwa na Apapa da Tin-Can Island a karkashin jagorancin shugaban Tashoshin Jiraghen Ruwan Nijeriya (NPA), Mohammed Bello-Koko, a Legas, Ministan ya kara da cewa, domin kaucewa tsayawar harkokin gudanawar tashoshin ya zama dole a gaggauta farfado da kayyakin da ke tashar don su ci gaba da aiki yadda ya kamata a kan haka ya nemi masu gudanar da ayyuka a tashar su tabbatar da ba hukumar NPA da gwamnatin tarayya goyon baya don a cimma wannan gaggarumin aiki na sabunta kayan aiki a tashar jiragen ruwa na Legas.
- Yadda Dakta Abubakar Tanko Bala Ya Zama Sabon Sakataren Kungiyar PACF
- Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah S.A.W (2)
Ministan ya kuma kara jadda cewa, “Domin kaucewa durkushewar ayyuka a tashar jiragen ruwan dole mu gaggauta sabunta kayan aiki a tashar jiragen ruwa na Apapa da Tincan Island sannan kuma ya kamata a ci gaba da shirin yashe tekun don ayyuka su ci gaba da tafiya yadda ya kamata.
“Na zagaya na kuma ga abubuwa da kaina, na yi taro da tattauanawa a cikin kwanaki 10 da suka wuce na kuma fahimci abubuwa da dama a kan haka nake kara jadda bukatar sabunta tare da bunkasa kayan aiki a tashoshin jiragen ruwanmu gaba daya.
“Kayayyakin duk sun nemi durkushewa, abin da na gani da ido na lallai ya kamata a sabunta kayayyakin tare da ci gaba da yashe teku.”
Tsohon gwamnan jihar Osun ya kuma yaba wa hukumar gudanarwa NPA, ya ce lallai suna bukatar goyon baya don a samu cimma abubuwan da ake bukata.
“Na yaba da yadda hukumar gudanarwar suke tafiyar da harkokinsu. Lallai ya kamata mu goya musu baya, ina kuma fatan masu gudanar da wasu bangarorin tashar za su bayar da nasu goyon bayan wajen farfado da tashar, goyon bayan su na da matukar muhimmanci don ta haka za su kara samun kudin shiga, haka kuma gwamnati za ta kara samun kudaden shiga, wannan lamari na hadin kai a tsakanin gwamanati da dukkan masu harkoki a ciki da wajen tashoshin gaba daya.
“Zamu fara wasu ayyukan gaggawa a tashar jirane ruwan, na bukaci a samar da cikakken rahoton yadda aikin zai gudana don mu san abin da aikin zai ci, don mu san kudaden da za mu nemi izinin kashe daga fadar shugaban kasa.
Tabbas muna da tsananin bukatar farfado da kayayyakin aiki a tashar domin ta haka ne zamu farfado ayyuka a tashar, ta haka ne kuma zamu samu karin kudaden shiga da bunkasa tattalin arzikin Nijeriya gaba daya. Muna tsananin dogaro ga mai amma kuma gashi a wannan bangaren akwai arziki sosai da ba a taba ba, dole mu mika godiya ga shugaban kasa a bisa yadda ya kirkiro wannan ma’aikatar.”
Ministan ya kuma ce, zai tuntubi ma’aikatar ayyuka don ganin yadda za a gyara hanyar da ta shiga tashar NPA. Daga karshe ya yi jinjina ga ayyuka da kokarin shugaban NPA Muhammed Bello Koko a kan yadda yake tafiyar da harkokin hukumar, ya kuma nemi ya kara kaimi domin akwai gaggarumnin aiki a gaba.
A nasa tsokacin, Shugaban NPA, Mohamed Belllo Koko ya mika godiya ga Ministan da tawagarsa a bisa ziyarar aiki da suka kawo, ya kuma yi alkawarin ci gaba da aiki yadda ya kamata.