Masu karatu assalamu alaikum wa rahmatullah. A wannan makon ma za mu ci gaba da darasi kan adalci, amana, kamewa da kuma gaskiyar Manzon Allah (SAW).
Kamar yadda muka tsaya a makon da ya gabata, Hiraklu – Sarkin Rum na wannan lokaci, ya tambayi Abu Sufyan da cewa, kun taba tuhumarsa da karya, Abu Sufyan ya ce, a’a, duk abin da ya tambaye ni ina ba shi amsa ta gaskiya sai abu daya da na yi zamba a ciki, Abu Sufyan ya ce wa sarki ba sa tuhumar Annabi (SAW) da laifin komai sai dai ya fada mana wata magana da mun rasa yadda za mu yi da ita.
- Juyin Mulki: Shugaban Kasar Gabon Ya Shaki Iskar ‘Yanci Bayan Hambarar Da Gwamnatinsa
- Zabe: Obi Ya Gaza Bayyana Yadda Ya Samu Kuri’u Masu Rinjaye – Kotun Zaben Shugaban Ƙasa
Sarki ya ce, wacce magana ce? Wata rana ya ce mana ya zo wannan gari kuma ya koma duk a dare daya.
Kuma mun san wannan tafiyar wata biyu ce zuwa da komawa, Ikon Allah, mai gadin Masallacin yana kusa, sai ya gasgata maganar Annabi (SAW), ya ce “A wannan daren, na kulle duk kofofin Masallacin amma daya ta ki rufuwa, na kira mutane su taya ni amma ta ki rufuwa, sai akace a bari da safe a kira magina su gyara kofar, da safe sai na ga alamar mutum ya shigo ya yi Sallah a ciki kuma na ga alamar huji a jikin bangon da Annabawa suke kulle abin hawansu in sun zo masallacin, sai na tabbatar cewa, lallai wani Annabi ya shigo masallacin”. Don haka, Rumawa babu abin da ba su sani ba game da Annabta.
Ikon Allah, da ma Sarki Hiraklu ya baro Rum ana ta jita-jitar cewa an ga tauraron sarkin masu Kaciya ya bayyana, sai sarki ya yi tambaya, su waye masu Kaciya? Aka amsa masa da cewa, Yahudawa ne, don haka mu kashe su kawai, ana cikin wannan takaddama sai dan aiken Annabi (SAW) ya kawo sakon Annabta, nan take sarkin ya ce a je a duba dan aiken a gani in yana da Kaciya, bayan tabbatar da dan aike yana da Kaciya, sai aka tabbatar cewa, wannan wasikar ce Allah ya nuna musu a tauraro.
Daga nan, sarki ya umurta a kai dan aiken Annabi (SAW), Duhyatu masauki, da dare ya yi, sarki ya nemi a kira dan aike, sai ya shiga da shi dakin ajiye asararan masarauta, Duhyatu ya ce, sai sarki ya dauko wata fata a nannade daban-daban, kowacce tana dauke da zanen Mutum a kanta, haka ya nuna mun hotunan Annabawa da yawa tun daga kan Annabi Adam har zuwa Annabi Muhammad (SAW), sai ya tambaye ni, waye ya turo ni a cikinsu? Sai na taba hoton Annabi (SAW), sannan ya kara dauko wasu hotunan mutum biyu daban a wani boyayyen wuri, sai na ga Sayyadina Abubakar da Umar, sannan ya nuna Umar ya ce shi zai karbe mulkinmu. Don haka, babu abin da ba mu sani ba, amma zan nuna maka wani abu, gobe da safe za a dawo da kai fada, da safe sarki ya sa aka zo da dan aike sannan ya sa aka tara masa masu-fada-a-ji na Daular Rumawa, sarki ya yi bayani da cewa, “Kun san an ba mu labarin dan aiken Ubangiji da zai zo wanda muna tsammani zai zo a cikinmu ne”, suka ce Eh, Sarki ya ce, “Allah ya bayyana shi amma ba a cikinmu ya zo ba, ga wasikarsa ta zo gare ni, kuma na yi Imani da shi.” Nan fa, manyan fada kowa ya tashi ya zura a guje, Kwamandojin Yaki suka fara shirin bore, daman sarki ya riga ya ba wa masu tsaron fada umurnin cewa, kar a bar kowa ya fita. Masu gadi suka kulle kofa, sannan sarki ya yi umurni da a dawo da su fada, sarki ya ce musu, “na gwada ku ne don in ga karfin imaninku, ina nan a kan addinina.”
Bayan an tashi zaman fada, sarki ya kira dan aiken Annabi ya ce masa, da odanunka ka ga abin da ya faru, wadannan mutane in na ce musu na bar addinina, to na rasa mulkina, amma ga sakona ga Annabi, ka ce “Na yi Imani da shi.” Wata ruwaya Annabi ya ce, karya yake yi, wata kuma ta bar hukunshi ga Ubangijinshi.
Nadru dan Harisu ya fada wa Kuraishawa, “Muhammadu tun yana Yaro yake cikinku, har ya zama saurayi mafi yarda a gare ku, mafi gaskiya, mafi aiki nagari, kuma mafi amana, har ya zo muku da abin da ya zo muku da shi duk ba ku ce mai Sihiri ba ne sai yanzu da har furfura ta fito masa! Waye zai yarda da ku? Wallahi ba mai Sihiri ba ne duk da cewa, shi ma Nadru bai yi Imani da Annabi (SAW) ba.
Ana cewa, ba wanda ya gasgataka ba ne almajirinka, wanda ya bi ka shi ne almajirinka. Da yawa na cewa “Mun gasgata shi amma babu ruwanmu da shi” kamar misalin Nadru.
Nadru, mafi sharrin mutum ne da ya fuskanci Annabi da munanan abu, yana daga cikin wadanda Annabi (SAW) ya sa aka fille wa kai bayan an dawo yakin Badr. Mafi yawancin maganganun kafirai da suka fada kan Annabi (SAW), Nadiru ne ya fade su. Shi ne mai zuwa kasashen Siriya ya siyo tatsuniyoyin mutanen farko yana karanta wa larabawa, yana cewa, Annabi (SAW) irinsu yake karantawa.
An karbo Hadisi daga Sayyada A’isha tana cewa “Annabi (SAW) bai taba shafar hannun macen da ba mallakinsa ba.” Malamai suka ce ya za a yi da Hadisin Anas da ya ce, kuyanga tana rike hannun Annabi (SAW) ta tafi da shi wurin biya mata bukatarta, kuma al’adar larabawa, suna gaisawa da ‘ya’yan Ammi.
Malamai suka ce, Hadisin Mubaya’a da mata suka yi masa a Fathu Makkah, Annabi (SAW) ya gaisa da Sayyadina Umar shi kuma Umar ya gaisa da matan. Don haka, Imam Abu Hanifa yana daya daga cikin wanda ya ba da fatawa, mace za ta iya gaisawa da wanda ba Muharraminta ba. Shehu Ibrahim Kaulakha (RA) ya yi bayani kan wannan mafita sosai a Tafsirinsa na (Suratul Mujadalah, ayar mubaya’a).
A cikin Hadisin Sayyadina Ali na Siffanta Annabi (SAW), yana cewa, shi ne mafi gaskiyar zance a mutane.
Ya fada a cikin Hadisi ingatacce, Annabi ya fada wa wannan mutumin da ya ce masa wannan rabo ba a yi adalci ba a cikinsa (Zulkhuwaisarah), Manzon Allah ya ce masa, kaiconka! Waye zai yi Adalci in ni ban yi adalci ba? Ashe na tabe kuma na yi asara in ban yi adalci ba!
Sayyada A’isha ta fada cewa, ba a taba ba wa Annabi (SAW) zabi cikin abu biyu ba face ya dauki mafi saukin ciki in dai ba zunubi ba ne, in kuma mafi saukin zunubi ne, Annabi (SAW) shi ne mafi nisanta daga gare shi.
Malam Abul’abbasil Mudarribu, ya ce, Sarkin Kisra ya raba kwanakinsa kamar haka: ranar da akwai Iska da Kura – bacci za a yi; ranar da gari ya rufe da Hadari – Farauta za a yi; ranar da ake Ruwan Sama – Giya za a sha sannan a yi wasanni; ranar da Rana ta fito – zaman Fada za a yi don biyan bukatun jama’a.
Dan Kalawaihi yake cewa, “Mamaki da yadda Sarakunan Kafirai suke shirya lamarin al’ummarsu” har yake cewa, Allah ya musu shaidar cewa, sun san zahirin rayuwar duniya amma rafkanannu ne ga lamarin Ubangiji. Don haka, Mumini ya kasa wani abu na lamarin Lahira shi ne ya ji kunya! Babu wata wayewa da Mumini zai yi, ya yi kafada da Kafiri a nan duniya, kowa da inda yake.
Annabi (SAW), ya raba ranarsa gida Uku: Na farko – Ibada; na biyu – Iyalinsa, na karshe – na kanshi ne. Sannan kuma sai ya sake raba kason kansa gida biyu, na farko ya bai wa kansa, na biyu ya bai wa jama’arsa.
Annabi (SAW) ya kasanace yana neman taimako daga kebantattunsa a kan jama’ar gama-gari da sauran jama’a, inda yake cewa, “ku wadanda kuke tare da ni, ku dinga fada min bukatun wadanda ba za su iya fitowa su zo wurina ba”. Duk wanda ya isar da bukatar wanda ba zai iya zuwa ya isar ba da kanshi, Allah zai amintar da shi a ranar tsoro (Lahira).