Da safiyar jiya Alhamis 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi tattaki zuwa jami’ar koyon aikin injiniya ta Harbin dake lardin Heilongjiang a arewa maso gabashin kasar, inda ya kara fahimtar tarihin ci gaban jami’ar gami da gudummawar da ta bayar ga sha’anin kimiyya da fasaha na tsaron kasa, da ganema idanunsa nasarorin da jami’ar ta samu a fannin koyarwa.
Xi ya kuma taya malaman dake jami’ar, gami da daukacin malaman kasar Sin, murnar ranar malamai, wadda za ta fada ranar Lahadi 10 ga watan Satumba. (Murtala Zhang)