Rundunar ‘yansandan Jihar Ribas ta cafke wasu ‘yansanda hudu da ake zargi da cin zarafin wasu mutane uku tare da karbar Naira miliyan 6.5 daga hannunsu.
An ce ‘yan sandan sun cafke mutanen ne ‘yan asalin Omoluwabi da ke Karamar Hukumar Ogba-Egbema-Ndoni ta jihar, ‘yansandan sun batawa mutanen suna ta hanyar kala musu karyar cewa wai ‘yan damfarar intanet ne, inda aka kai su Jihar Delta suka tsare kuma suka kudin daga hannunsu bayan sun tsare su na tsawon kwanaki biyu.
- Hajjin Badi: Dalilin Kara Kudin Kujera Zuwa Naira Miliyan 4.5 – NAHCON
- Firaministan Sin Ya Bukaci Taron Kolin Gabashin Asiya Da Ya Inganta Zaman Lafiya Da Wadata A Yankin
An gano cewa ‘yansandan sun kama mutanen ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2023, sannan suka sake su a ranar 1 ga Agusta, 2023.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Emeka Nwonyi, yayin da yake gabatar da ‘yansandan a gaban ‘yan jarida a Fatakwal, ya ce yana bakin kokarinsa wajen ganin ya kawar da bara gurbi.
Nwonyi ya ce, “Kuna iya ganin wasu jami’an ‘yansanda. Sama da mako biyu kenan a tsare saboda wani laifi, sun aikata laifin bisa radin kansu, mu kuma mun kama su don mu nuna cewa muna nan kan aikinmu na ganin mun tsarkake kanmu.
“Ba na jin akwai wata hukuma kamar hukumar ‘yansanda wajen tsaftace al’umma da kokarin fitar da marasa gaskiya daga cikin al’umma a cikin tsari.”
Sai dai shugaban ‘yansandan bai bayyana sunayen ‘yan sandan ba.
Hakazalika, Nwonyi ya gabatar da wasu ‘yansanda hudu da suka hada da Sufetoci uku da aka kama bisa zargin cin zarafin wata dake kan hanyar balaguro.
Ya ce ‘yansandan sun yi ta kai farmaki ne a lokacin da suka yi wa matar fyade a kusa da ‘Arcania Junction’, Ada George Road a Fatakwal ranar Lahadi.
Agba Emmanuel, da wasu mutane uku da suka hada da sufeta Abgani Peter, sufeta Ozenewa Amadi da Sargeant Akuigbo Bartholomew.
“An kama su duka kuma suna tsare ana yi musu tambayoyi.
“Har ila yau, ina kira ga matar da aka ci zarafinta da ta zo ofishina ta ba mu bayanan bangarenta game da lamarin domin a gudanar da bincike mai inganci.”