Jami’an tsaron Cibil Defence na Nijeriya reshen babban birnin tarayya, sun kama wasu mutum uku da ake zargi da aikata satar manyan wayoyi mallakar kamfanin sadarwa.
Wadanda ake zargin su ne Peter Kile mai shekara 27 daga Karamar Hukumar Bandeikya ta Jihar Benue; Akanuge Sammel mai shekara 27 daga Karamar Hukumar Konshisha ta Jihar Benue; da Justin Tundu mai shekara 31 shima daga Karamar Hukumar Konshisha.
- Share Fagen Gasar Kofin Duniya; Messi Ya Zura Kwallo A Ragar Ecuador
- Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah S.A.W (2)
A cewar mai magana da yawun rundunar, Comfort Okomanyi, an kama wadanda ake zargin ne a kusa da gidan da ke mahadar cocin Rock, titin filin jirgin sama a Abuja da wayoyin fiber da aka gano mallakar gwamnati ne.
Rundunar NSCDC dake sintiri a babban birnin tarayya ta ce ta kama wadanda ake zargin ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa wasu miyagu sun yi shiga irin ta injiniyoyi da aka tabbatar da barayin wayoyi ne mallakar kamfanin sadarwa na kasa ne.
Okomanyi ya nakalto cewa Kwamandan Babban Birnin Tarayya, NSCDC, Olusola Odumosu, ya yi alkawari yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin cewa, ba za su taba yarda da irin wannan barna.
Ya ce “Za mu kori barayi daga FCT. Kun fara ganin sakamakon ayyukan da jami’anmu na sintiri ke yi. Za mu kara himma wajen kamun duk wani mai laifi, kuma za a kara kama wasu nan gaba kadan.
“Wadannan mutane uku da ake zargi sun lalata tare da kwashe wayoyin fiber, amma abin takaici a gare su, mutanen da ke sa ido na a wurin sun dakile shirinsu.”