Kungiyar Miyetti Allah ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Jihohi da su yi la’akari da ’ya’yanta makiyaya wajen rabon kayan abinci don rage radadin da ke tattare da cire tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kwara, Alhaji Bello Abubakar, ne ya yi wannan kiran a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin.
Abubakar ya bayyana makiyaya a matsayin wadanda cutar ta fi shafa a wannan lokaci.
Shugaban ya bayyana cewa, galibin makiyayan ba su da asusun ajiya a banki inda za su iya samun kudade cikin sauki a lokacin da suke bukata.
A cewarsa, a duk lokacin da makiyaya suka kai dabbobinsu kasuwa domin sayarwa, suna kashe kudin sufuri mai yawa cikin kudin.
Shugaban Fulanin ya nuna damuwarsa kan tsadar kayan abinci a kasuwa.
Ya yi kira ga gwamnati da ta saki kayan abinci daga asusun ajiyar kasa tare da bayar da tallafin kudade ga talakawan Nijeriya.
Abubakar ya kuma bukaci gwamnati da ta taimaka wa mambobinsu da alluran rigakafi don rage yawaitar mutuwar dabbobinsu daga cututtuka.
Ya kuma gargadi masu aikata miyagun laifuka a tsakanin Fulani da su yi watsi da aikata laifuka da sauran munanan dabi’u domin amfanin kansu.
Baya ga haka, Abubakar ya shawarci makiyaya da manoma da su rungumi tsarin tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummominsu daban-daban.