Kamfanin Apple ya shirya tsaf a yau Talata, 12 ga watan Satumba don bayyana sabbin nau’ukan wayar iPhone 15
A baya LEADERSHIP ta bayar da rahoton cewa, kamfanin Apple zai gudanar da bikin shekara ta bana a ranar Talata 12 ga watan Satumba.
A yayin bikin, kamfanin ya ke fitar da sabuwar iPhone duk shekara kuma ana sa ran zai fitar da nau’ukan iPhone 15 guda hudu.
Talla
A cewar Bloomberg’s Mark Gurman, wanda ke fitar da ingantaccen shirin kamfanin Apple, ya bayyana cewa, an inganta iPhone 14 zuwa iPhone 15 da iPhone 15 flos.
Talla