Annabi (SAW), ya raba ranarsa gida Uku: Na farko – Ibada; na biyu – Iyalinsa, na karshe – na kanshi ne. Sannan kuma sai ya sake raba kason kansa gida biyu, na farko ya bai wa kansa, na biyu ya bai wa Jama’arsa.
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana neman taimakon kebantattunsa daga gama-gari, inda yake cewa, ku wadanda kuke tare da ni, ku dinga isar min da bukatar wadanda ba za su iya isowa gare ni ba da bukatarsu. Yadda abun yake shi ne, duk wanda ya isar da bukatar wani wanda ba zai iya isar da ita ba, Allah Ubangiji zai amintar da shi ranar tsoro babba (Ranar Alkiyama). Misali, Mutum ba zai iya isar da gaskiyarsa a kotu ba, to Lauya ya isar masa. Sabida, wani in ya je kotu da gaskiyarsa sai ya gigice ya kasa bayyana ta, to Lauya mai gaskiya ya isar masa.
An karba daga Hassan, Dan Sayyadina Ali (RA) yana cewa, Manzon Allah (SAW) ya kasance, ba ya rike wani mutum daya da kagen wani. Don wani ya kitsa karya a kan wani mutum, Annabi (SAW) ba ya kama mutum da ita har sai ya yi bincike a kanta. Sannan kuma bai gasgata maganar wani a kan wani har sai ya yi bincike gaskiya ta bayyana.
Abu Ja’afaril Dabri ya fitar da Hadisi, daga Sayyadina Ali daga Annabi (SAW) yana cewa, “ban taba himmar aikata wani abu daga abin da ‘yan jahilyya suke aikatawa da shi ba sai sau biyu, amma dukka guda biyun sai Allah ya tsare ni daga aikatawa, har Allah ya girmama ni da aikensa”. Abubuwa biyun su ne:
Na farko: Wata rana Annabi (SAW) yana kiwo a wajen garin Makkah tare da wani Yaro, sai ya ce wa yaron da za ka kula min da tumakina in shiga cikin garin Makkah ni ma in dan shakata kamar yadda sauran samari suke shiga, sabida kullun muna cikin dajin kiwo, sai yaron ya amince, ni kuma na shirya, har sai da na zo gidan farko na shiga garin Makkah, sai na ji ana buga ganga da algaita sabida wani aure da ake yi, sai na zauna ina kallo, sai Ubangiji ya yi rufi a kunnena na daina jin komai (ya yi bacci), ban farka ba har sai da hasken rana ya tashe ni. Ban kewaya a gari ba, ga shi na bar tumakina.
Na biyu: shi ma irin na farko ne, amma Allah ya kawo wani abu shi ma na yi bacci. Daga nan, na ce ba zan kara zuwa ba tun da ban da rabo cikin irin wadannan abubuwan.
Shi Mumini duk lokacin da ya yi yunkurin aikata wani abu da shari’ar musulunci ba ta yarda da shi ba, sai Allah ya tona asiri amma wanda ba Mumini ba sai ya dade yana aikata barna Allah bai tona masa asiri ba sabida Allah babu ruwanshi da shi.
Sabon Darasi da zai yi Magana kan Nutsuwa da Mutuntaka (Daddaku) ta Annabi (SAW).
Game da Nutsuwar Manzon Allah (SAW) da Kawaicinsa da kuma rashin gaggawa (yin abu a sannu-sannu) da mutuntakarsa da kyakkyawar shiryarwarsa, Umar bin Abdulaziz bin Huwair ya ce, ya ji Harisata dan Zaidu yana cewa, Annabi (SAW) ya kasance mafi nutsuwar mutane a mazauninsa, ba za ka ji wani abu ya fito daga cikin Annabi (SAW) ba kamar Kaki, Ballan Kashi, Tusa da dai sauransu in yana zaune cikin Jama’a amma in ya koma gida yakan sakin jikinsa.
Abu Sa’idil Kuduri ya ruwaito hadisi yana cewa, Manzon Allah (SAW) ya kasance idan ya zauna a mazauni sai ya yi ihkaba’i (wani irin tsarin zama ne da Larabawa ke kulle gabobinsu da gobobinsu, sabida mutane ne a Sahara, ba su da Bango na jingina), Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi yawancin tsarin zamansa, Ihkaba’i.
An karba Hadisi daga Jabir dan Samurata, ya ce Manzon Allah (SAW) yana harde Kafarsa wurin zama, da yawa yake zaman Kurfasa’u. Manzon Allah (SAW) ya kasance mai yawan shiru in ba karatu yake yi ba, da yawa yake kauda kai ga wanda ya yi magana wacce ba ta dace ba a tsakiyar zance. Dariyar Annabi (SAW) ta kasance murmushi ce, wani lokacin yakan yi dariya har Turamen hakoransa su bayyana, Kalamansa a rarrabe suke – Hikima ce cikakkiya ba cakudin magana ba, Mai yawan Zikiri ne ba ya magana sai in ta dace, dariyar Sahabbansa a gabansa murmushi ce don koyi da kuma girmamawa a gareshi.
Mazaunin Manzon Allah (SAW), mazauni ne na karatu da hakuri da kunya da alkhairi da amana, ba a daga muryoyi a mazauninsa wacce za ta zama ta rashin ladabi, ba a keta alfarmar mai alfarma a mazauninsa, idan yana magana da sahabbansa ka ce tsuntsu ne a kan kafadunsu sabida nutsuwa.
Yana daga cikin abubuwan da aka ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) in yana tafiya, tafiyarsa kamar ciccirawa yake yi da kuzari amma a natse, in yana tafiya, kamar yana saukowa daga tudu, sahabbai sai sun hada da gudu shi kuma tafiya dai-dai yake yi. Don haka, sahabbai ke cewa, suna zaton ana nade masa kasa ne wurin tafiya.
A wani hadisi kuma, ya zo cewa, idan Annabi (SAW) yana tafiya, tafiya yake yi baki daya ba rangaji ko rangwada ba. Ana gane Annabi a tafiya cewa, ba ya tafiyar gajiyayyu ko tafiyar kasalallu.
Abdullahi bin Mas’ud ya ce, mafi kyawun shiryarwa dai, ita ce shiryarwar Annabi Muhammadu (SAW).
An karba daga Jabiru, Allah ya yarda da shi ya ce, akwai Fasaha (rarrabe magana) a cikin maganar Annabi Muhammad (SAW).
Dan Abi Halata yake fada cewa, Shirun Annabi (SAW) ya kasu gida Hudu:
Akwai shirun hakuri – wani ya yi wauta, yana da ikon da zai sa a sare masa kai amma sai ya yi shiru don kar ya fada wata magana ta zama hukunci kuma ga masu zartaswa a kusa.
Akwai shirun taka-tsan-tsan – kar Annabi (SAW) ya yi magana ta zama hatsari sabida irin wurin da ake, da irin mutanen da ake cikinsu (mutanen za su iya daukar sirrin ko ba za su iya ba).
Akwai shiru na cikin girmansa – akwai maganar da ba ta kai Annabi (SAW) ya tanka ba, wani in ka mayar masa da magana ka girmama shi.
Akwai shirun tunani cikin Allah – Manzon Allah (SAW) kullum cikin tafakkurin Ubangiji yake, don haka yake Istigfari, in an kai mataki na gaba sai a fahimta. Annabi (SAW) kullun ci gaba yake da tafiya a Hadarar Ubangijinsa.
Sayyada A’isha (RA) ta ce, Annabi (SAW) ya kasance yana zantar da zance, da mai kirgawa zai kirga kalmomin zancen, da sai a ga kalmomin da Annabi ya yi amfani da su sabida rarrabe zance da rashin sauri a ciki.
Wata rana Abi Hurairah yana bayar da Karatu, sai ya ji Sayyada A’isha tana Sallah a bayanshi kuma kamar tana sauri ta idar, sai Abi Hurairah ya fahimci sabida shi take sauri, sai ya yi sauri ya wuce, bayan ta yi sallama, ta tambaya ina yake? Aka ce, ya wuce, sai ta ce, ba karyata shi zan yi ba amma yadda yake karatu da sauri-sauri ba haka Annabi (SAW) yake yi ba.
Manzon Allah ya kasance yana son Turare da kamshi mai dadi, kuma yana amfani da duk wani abu mai kamshi, yana kwadaitarwa akan Turare, yana cewa “a cikin duniyar nan taku, an soyar min da Mata in auresu don halas sai kuma Turare, an sanya sanyin idanuna a cikin Sallah, ba na nutsuwa sai na tayar da Sallah.”