Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya kai karar shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas gaban Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa daukaka dan majalisar jiharsa, Ikenga Imo Ugochinyere wajen ba shi kwamiti mai gwabi a cikin gwamnatin jam’iyyar APC.
Uzodinma ya bayyana rashin jin dadinsa ga Abbas wajen martaba Ugochinyere, wanda ya kasance dan majalisa a karkashin tutur jam’iyyar PDP, na danka masa shugabancin kwamitin man fetur (da aka tace).
An bayyana cewa Uzodinma wanda ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin APC ya kalubalance nadi bokin hamayyarsa shugaban kwamitin majalisa mai gwabi tun loacin da aka sanar da nadin.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa shugaban majalisar wakilai Abbas ya fusata Uzo-dinma wanda yake ganin cewa wannan nadin zai bai wa Ugochinyere shahara a cikin harkokin siyasa.
Bayan haka kuma, an bayyana cewa gwamnan ya dauki nadin dan majalisar a matsayin shugaban kwamitin mai gwabi za sa dan adawa ya kara karfi a siyasance, wanda hakan cin mutunci ne a matsayinsa na gwamnan jihar kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC.
Wata majiya da ke kusa da gwamnan ta bayyana cewa, lallai gwamnan ya yi matukar fusata da nadin Ugochinyere wanda hakan zai taba kimarsa a matsayinsa na gwamnan Jihar Imo.
A cewar wata majiyar, Uzodinma ya damu sosai na nadin Ugochinyere shugabancin kwamitin mai gwabi a zauren majalisar wakilai na tarayya, wanda hakan zai kara wa ‘yan adawa karfi a cikin harkokin siyasa.
Duk da dai kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Jihar Nasarawa ta soke zaben Ugochinyere, dan majalisar ya daukaka kara na kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Ugochinyere zai ci gaba da zama dan majalisar wakilai har sai kotun daukaka kara ta zantar da hukunci.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Uzodinma ya yi kokarin shawo kan Abbas kan ya janye nadin.
An samu rahoton da ke cewa shugaban majalisar wakilan ya yi watsi da bukatar gwamnan.
LEADERSHIP ta kuma kara da cewa tuni Uzodinma ya kai karar Abbas gaban Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan wannan nadin.
Har ila yau, a nasa martanin, Ugochinyere ya bukaci Uzodinma ya cire Abbas daga ciki siyasar Jihar Imo.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, dan majalisar da ke cikin rudani ya bayyana cewa ba sai ya bukaci goyon bayan Abbas ba wajen murkushe Uzodinma a zabe mai zuwa a jihar.
Ya siffanta Uzodimma a matsayin karamin kwaro a siyasa. Ya ce, “Za mu mur-kushe Uzodinma a zaben gwamna a watan Nuwamba kamar yadda muka yi a zaben watan Mayu.”