A yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, an tambayi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, game da rahoton da shugaban Amurka Joe Biden ya mikawa majalissar dokokin kasar sa, wanda a ciki ya ayyana Sin a matsayin ginshikin yaduwar miyagun kwayoyi. Game da hakan, Mao Ning ta ce Amurka ba ta gabatar da wasu shaidu na hakika ba, kuma batu ne mai kunshe da mummunar manufa.
Mao Ning ta kara da cewa, tushen yaduwar miyagun kwayoyi a Amurka, na da nasaba ne da gazawar jagorancin kasar, kuma dakile bukatar kwayoyin a cikin kasar shi ne jigon shawo kan matsalar.
A daya bangaren kuma, jami’ar ta ce a baya bayan nan, majalissar dokokin nahiyar tsakiyar Amurka, ta amince da wani kuduri na soke matsayin ‘yar sa ido ta dindindin na “majalisar dokoki” ta yankin Taiwan, kana majalissar ta amince a baiwa majalisar wakilan jama’ar kasar Sin kujerar dindindin ta sanya ido. Dukkanin wadannan kudurori, kasar Sin ta yi matukar maraba da su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)