Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa (IPC) da cibiyar kare hakkin ‘yan jarida (I-CSPJ) da ke da reshe a jihar Legas ta yi allawadai dangane da yadda wasu jami’an ‘yansanda suka muzguna ma wasu ‘yan jarida a lokacin da suke bakin aikinsu na dauko rahoton shari’ar kujerar gwamnan Kano da aka gudanar a ranar Laraba.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da ta fito mai dauke da sa hannun jami’in I-CSPJ Melody Akinjiyan wadda aka aike wa ‘yan jaridu.
Sanarwar ta bayyana sunayen ‘yan jaridar da aka kai wa harin da Salim Umar Ibrahim na Daily Trust da kuma wakilin BBC Hausa, Zahraddeen Lawal.
Rahoto da ya fito daga bakin Salim Ibrahim na gidan jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, ‘’’Yansandan da ke bakin aiki sun bukaci ‘yan jaridan da su yi nesa da harabar kotun kimanin nisan mita 10, ana cikin haka ne kawai sai wasu daga cikin ‘yansandan suka dirar wa ‘yan jarida wai suna daukar hoto.
“Sannan kuma suka bi ma’aikacin BBC, inda suke kokarin kwace masa wayarsa, wasu kuma daga cikinsu suka farwa Salim Ibrahim na jaridar Daily Trust inda suka karbe masa wayarsa ta karfin tsiya, tare da lalata masa wayar,” cewar rahoton.
Babban Darakta IPC, Mista Lanre Arogundade ya ce, “Harin ba gaira ba dalili da ake kai wa ‘yan jarida a bakin aikinsu babbar kalubale ne da wukakanta dimokuradiyyar mu kuma a wurin mu babbar barazana ce ga ‘yancin ‘yan jarida. Irin wannan hukuncin ya saba wa hakkokin ‘yan jarida.”
Sannan cibiyar ta bukaci rundunar ‘yansandan Nijeriya da su bi a hankali game da irin matakan da suke dauka a kan ‘yan jarida, domin hakan na iya haifar da tsoro ga ‘yan jarida ya yin gudanar da ayyukan su.
Melody Akinjiyan ta kuma ce cibiyar ta yi kira ga kwamishinan ‘yansandan jihar Kano da ya dauki kwakkwaran matakai da suka dace don ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tsaurara matakai wajen ganin an biya wadanda aka ciwa zarafi diyya.
Ta kuma yi kira ga jami’an ‘yansanda da su kasance masu ba wa ‘yan jarida hadin kai.