• English
  • Business News
Saturday, September 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Japan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yau ne ake cika wata guda da fara zubar da dagwalon tashar Nukiliyar Fukushima ta Japan a cikin Tekun Pacific, lamarin da ya haifar da tir da Allah-wadai da kuma fargabar illar da abin zai yi ga rayuwar bil’adama a doron kasa da kuma halittun da ke cikin ruwa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne firaministan tsibiran Solomon Manasseh Sogavare ya yi Allah wadai da zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku, ya bayyana hakan a matsayin wani hari kan amana da hadin kan duniya. “Rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ba ta cika ba, kuma bayanan kimiyyar da aka fitar ba su wadatar ba, kuma suna cike da son zuciya, yayin da aka yi watsi da wadannan damuwar,” a cewar sa. Firamininstan ya ci gaba da cewa, Idan ruwan dagwalon nukiliyar ba ta da hadari, kamata ya yi Japan ta adana ruwan a kasarta, kasancewar an zubar da ruwan dagwalon a cikin teku na nuni da cewa tana da hadari.

  • Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Hukumar Kula Da Hakkin Bil Adam Ta MDD Kan Batun Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Ta Japan
  • Me Ya Sa Amurka Ke Goyon Bayan Matakin Japan Na Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku?

Dagwalon da Japan ke zubarwa da adadinsa ya haura sama da tan miliyan daya daga ranar 24 ga Agustan 2023, ana iya shafe kimanin shekara 30 ana yi ba a kammala ba.

Adawa da abin da Japan ke yi daga masu ruwa da tsaki kan sha’anin teku ya tabbatar da kin amincewa da ikirarin gwamnatin kasar na cewa an tsaftace dagawalon. Daga cikin gida, wani gungun mazauna kasar a karkashin Majalisar Hulda da Jama’a ta kasa da ke adawa da zubar da dagwalon masana’antun makamashin nukiliya, sun shigar da kara a ofishin Gundumar Tokyo. Inda suka zargi Firayim Minista Fumio Kishida da Shugaban Kamfanin Lantarki na Tokyo (TEPCO) Mista Tomoaki da nuna sakaci kan wannan al’amari.

Masu koken sun bayyana cewa dagwalon na dauke da makamashi mai guba baya ga sinadarai masu hadari da ke narkewa wanda ba zai yiwu a raba shi da dagwalon ba ko da bayan an tsaftace shi. Suka kara da cewa har yanzu wannan babbar barazana ce ga kiwon lafiyar dimbin mutanen da suke cin naman dabbobin ruwa.

Labarai Masu Nasaba

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Har ila yau, akwai masana kimiyya da suka nuna shakku game da rashin hadarin dagwalon da Japan ke zubarwa. A rahoton da Kungiyar Masu Zurfafa Binciken Kimiyya ta Amurka da ke Birnin Washington, ta wallafa a 2021, ta ce akwai yiwuwar a samu wasu sinadaran makamashi masu guba da ke daukar tsawon lokaci ba su narke ba, da za su iya silalewa yayin gudanar da aikin tsaftace dagwalon.

Bugu da kari, a mukalar da ya rubuta, mai taken “Shin dagwalon Fukushima ba shi da hadari? Abin da kimiyya ta ce” da aka buga a Mujallar “Nature” cikin watan Yuni, masanin halittun ruwa, Mista Robert Richmond daga Jami’ar Hawaii ya yi tambaya: “Shin mutanen da ke sahihantar da wannan (fitar da dagwalon makamashin nukiliya na Japan)… sun nuna gamsuwarmu ne cewa zai kasance ba tare da wani hadari ba ga lafiyar Dan’adam da kuma teku? “Amsar ita ce a’a,” in ji Richmond.

Shi ma daya daga cikin masana kimiyya biyar na kwamitin ba da shawara ga Dandalin Tsibiran Pasifik, Richmond ya ce bayan nazarin bayanai daga Kamfanin Lantarki na TEPCO da Gwamnatin Japan, da kuma ziyartar tashar nukiliyar Fukushima, ba a magance zargin da ke cikin fitar da dagwalon ba.

Bisa bayanan masanan, zubar da dagwalon a teku zai haifar da mummunar illa ga muhalli da za a dade ba a magance ba, sakamakon makamashi da sinadarai masu hadari ga halittun ruwa da ‘yan adam musamman masunta da mutanen garuruwan da ke gabar teku.

Bayanai na nuna cewa damuwar da aka shiga kan zubar da dagwalon ta jefa shakku a zukatan mutane musamman wadanda ke zama a kusa da tashar Fukushima game da abin da gwamnatin Japan ke yi, sakamakon har yanzu ba su manta da yadda aka yi tafiyar hawainiya wajen sanar da su bayanan da suka kamata ba bayan ibtila’in da ya auku a 2011.

Masu kare hakkin Dan adam na Majalisar Dinkin Duniya su ma sun nuna adawa da abin da Japan ke yi, haka su ma masu rajin kare lafiyar muhalli. Kungiyar Kare Lafiyar Muhalli ta Greenpeace ta fitar da rahotannin da suka nuna shakku a kan matakan da Kamfanin TEPCO ke amfani da su wajen tsaftace dagwalon, inda ta yi zargin cewa ba a zurfafawa ta yadda za a magance illar da abin ka iya haifarwa.

Ita ma Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta da zubar da dagwalon na Japan a teku. Rahotanni sun nuna cewa tuni kasar ta dauki matakin rage yawan abincin da ake samu daga teku da kasar ke sayowa daga Japan. A kasar Koriya ta Kudu ma, wani sauraron ra’ayoyin jama’a da aka gabatar kwanan baya, ya nuna kashi 80 cikin 100 na mutanen kasar sun nuna damuwa kan fitar da dagwalon.

Wasu na iya tunanin cewa, watakila Japan ba ta da zabi ne illa ta antaya dagwalon a teku, sai dai kuma ba haka ba ne. Wani babban masanin kimiyya a Cibiyar Binciken Kimiyyar Teku da Muhalli ta Woods Hole Oceanographic da ke Birnin Massachusetts na Amurka, Mista Ken Buesseler, ya ce kamata ya yi Japan ta zubar da dagwalon a kan-tudu, “domin zai fi saukin sa ido da kula da abubuwan da ka iya haifarwa.” Haka nan da an hada da zabin gauraya dagwalon da kankare wajen fitarwa.

Matukar kasashen duniya suka rungume hannu suka bari wannan dabi’a ta Japan ta ci gaba, tabbas kilu za ta jawo bau, domin kamar yadda Mista Buesseler ya nuna fargaba a kai, abin da Japan ke yi na iya bude kofa ga wasu kasashe ta zubar da dagwalon nukiliyarsu a teku. Riga-kafi dai ya fi magani!

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dagwalon NukiliyaJapan
ShareTweetSendShare
Previous Post

Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya Da Suka Fafata Yakin Biyafara

Next Post

Kungiya Ta Nemi ‘Yan Adawa Su Rungumi Kaddara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Bauchi

Related

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya
Daga Birnin Sin

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

1 hour ago
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

2 hours ago
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin
Daga Birnin Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

3 hours ago
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin
Daga Birnin Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

4 hours ago
Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka
Daga Birnin Sin

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

5 hours ago
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154
Daga Birnin Sin

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

6 hours ago
Next Post
Gwamna Bala

Kungiya Ta Nemi 'Yan Adawa Su Rungumi Kaddara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

September 12, 2025
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

September 12, 2025
Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

September 12, 2025
Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

September 12, 2025
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

September 12, 2025
Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

September 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.