Dakarun sojoji na musamman na rundunar hadin guiwa da ke aiki a shiyyar Arewa maso Yamma a karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya, sun sake ceto wasu mutane 15 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.
An ceto mutanen ne a ranar Litinin, 25 ga Satumba, 2023, a kauyen Kayan Boggo da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar.
- Sojoji Sun Ceto Wasu Karin Dalibai Mata 7 Na Jami’ar Tarayya Da Ke Gusau Jihar Zamfara
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
A cewar Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya ce, bayan samun bayanan sirri, sojojin sun tare wata hanya da ake zargin ‘yan ta’addan na amfani da ita in sun sato mutane.
Ya ce, “sojojin sun kashe ‘yan ta’addan da dama da suka fada tarkonsu, lamarin da ya tilasta musu tserewa suka bar mutanen da suka sato”.
“Majiyoyin soji sun ce, an mika wadanda aka tsiratar ga hakimin Gwashi domin hada su da iyalansu.”
A baya LEADERSHIP ta rahoto cewa, an kubutar da dalibai mata 13 cikin sama da 20 na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS), wadanda ‘yan bindiga suka sace a wani dakin kwanan dalibai da ke garin Sabon Gida a karamar hukumar Bungudu ta jihar a ranar Juma’a.