• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Somaliya Da ATMIS Sun Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Tsakiyar Kasar

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
ATMIS

Mahukuntan Somaliya da tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka ko ATMIS a takaice, sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da ‘yan ta’addar Al-Shabab suka kai a birnin Beledweyne dake tsakiyar Kasar Somaliya, harin da ya haddasa mutuwar mutum a kalla 20 tare da jikkata wasu da dama.

A sanarwar da Shugaban Kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, da Mohammed El-Amine Souef, wakilin musamman na shugaban hukumar gudanarwar AU a Somaliya, kana shugaban ATMIS suka fitar daban-daban, sun lashi takobin kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, duk da karuwar hare-haren da kungiyar ta’addanci take kaddamarwa.

  • A Shirye Sin Take Ta Inganta Hadin Gwiwa Da UNESCO Domin Samar Da Ci Gaba Da Zaman Lafiya A Duniya
  • Xi Ya Karfafawa ‘Ya‘yan Wadanda Suka Sadaukar Da Rayuwarsu Da Su Zama Amintattu Masu Kare JKS Da Al’umma

Haka kuma, shugaba Mohamud ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.

Wani dan kunar bakin wake ne dai ya tayar da nakiya a cikin wata babbar mota makare da bama-bamai a wani shingen binciken jami’an tsaro dake kusa da wata kasuwa da gidajen mai guda biyu a birnin Beledweyne dake yankin Hiran.

Rahotanni na cewa, an garzaya da wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ta jirgin sama zuwa Mogadishu, babban birnin Somaliya, domin samun kulawa ta musamman.

LABARAI MASU NASABA

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

A nasa bangare, Mohammed El-Amine Souef ya ce, harin da aka kai kan fararen hula da ba su ji ba su gani ba, an yi shi ne da nufin karkatar da hankalin jama’a dangane da gagarumar asarar da kungiyar al-Shabab ta tabka a hare-haren da gwamnati ke ci gaba da kaiwa da nufin murkushe su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump
Labarai

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya
Manyan Labarai

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Next Post
Uwargidan Gwamna Ta Jagoranci Tattaki Kan Yaki Da Cutar Sikila A Jihar Zamfara

Uwargidan Gwamna Ta Jagoranci Tattaki Kan Yaki Da Cutar Sikila A Jihar Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.