Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na Girki Adon Mata.
Abubuwa da Uwargida za ta tanada:
Kifi, fafirika, fulawa, kwai, yis, mai, albasa, magi, gishiri, kayan kamshi:
Da farko za ki wanke kifin sannan sai ki yi kamar ganishin dinshi wato za ki dan tsatstsaga tsakiyar sa kadan-kadan saboda kayan hadin ya shiga cikinsa, sai ki dan barbada masa fafirikan sannan ki dan barbada masa magi da gishiri da kayan kamshi sai ki shashshafa a jikin kifin, sannan ki juya kasan shima ki shashshafa ko ina ya zama ya samu ya shisshiga cikin kifin inda kika tsatstsaga sai ki yanka albasa kanana ki barbada a saman kifin sannan sai ki dan barbada mai a sama, sai ki sashi a obon ki kunnan masa wuta ki barshi ya kasu kafin ya kasu sai ki kwaba fulawa, idan kika zuba fulawar a wata roba sai ki zuba yis sannan ki zuba gishiri sannan ki kawo dan mai ki zuba, ki zuba ruwa mai dan dumi ki kwaba, za ki kwaba da dan tauri kamar kwabin cincin sai kibarshi ya yi kamar minti goma saboda ya dan tashi kafin nan kifin ya gasu, sai ki fitar da kifin ki barshi yadan huce.
Daga nan ki dakko wannan kwabin fulawar, ki samu cafin bot sai ki dan barbada fulawa a samansa sannan ki raba wannan kwabin naki biyu sai ki dora daya akan cafin bot din ki tada shi daidai yadda za ki rufa a saman kifin sai ki dakko dayan shima ki tada shi kamar yadda kika tada dayan sai ki daga wannan kifin ki dora shi akan guda daya, dayan kuma ki rufa shi a saman kin ga kin rufe kifin, sai ki kama bakin na kasa da na sama ki rurrufe shi ki mammane shi ko ina ya rufe haka za ki gewaye shi tun da kifin yana ciki kuma ya rufe shi gaba daya.
Sannan ki fasa kwai ki dan sa masa gishiri kadan sai ki shafe shi da kwan ki maida shi cikin obon ki kunna wutar sama da kasa ya kasu. Habba mana Uwargida ya kika ga kifin nan ranar mai gida babu futa hira.