Bayan dogon hutu na watanni uku, an sake bude makarantun boko a Jamhuriyar Nijar, yayin da kasar ke ci gaba da fadi-tashin yadda za ta tunkari kasashen kungiyar ECOWAS da ke barazanar tura mata dakarun soji.
To sai dai komawa makarantar a wannan karo, ya zo ne a cikin wani yanayi, sanadiyyar takunkuman da aka kakaba wa kasar bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokuradiyya.
- Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo
- Tawagar Masu Aikin Na’urar Binciken Duniyar Wata Mai Suna Chang’e 5 Ta Kasar Sin Ta Samu Babbar Lambar Yabo
A ranar 26 ga watan Yuli aka wayi gari da labarin cewar sojojin da suke tsaron fadar shugaban kasa, a karkashin jagorancin Janar Abderahmane Tchiane sun tsare shugaba Bazoum a cikin fadarsa, abin da ya jefa fargaba a ciki da wajen kasar.
Daga bisani, sojojin sun yi sanarwar kawar da shugaba Bazoum da kuma tsare shi tare da wasu ministocinsa saboda wasu dalilai da suka bayar wanda ya shafi tsaron kasa da kuma irin barazanar da Nijar ta ke fuskanta.
Kazalika sojojin sun sha suka daga kasashe da dama kan tsare shugaba Bazoum ciki har da mukarrabansa.
Kazalika, ECOWAS ta yi yunkurin daukar matakin soji a kan sojojin da suka kifar da gwamnatin dimokuraddiya a kasar.
Sai dai al’amura na ci gaba da daidaita yayin da gwamnatin sojin kasar ke neman sake kulla alaka da wasu kasashe.