Fadar shugaban Nijeriya a karon farko, ta yi watsi da zargin da ake yi cewa takardar shaidar kammala karatu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bogi ce.Â
Idan dai ba a manta ba, a cikin wannan makon ne Jami’ar Chicago da ke kasar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu, bayan umarnin wata kotun kasar a hukuncin da ta yanke kan karar da dan takarar jam’iyar PDP a zaben da ya gabata na 2023, Atiku Abubakar, ya shigar don samun karin hujja game da zargin sahihancin takardun karatunsa.
- Jami’ar Danfodiyo Ta Musanta Harin ‘Yan Bindiga A Harabar Jami’ar
- Arsenal Ta Yi Rashin Nasara A Karon Farko A Bana
Duk da cewar takardar shekarar karatun Tinubu da jami’ar ta Chicago ta fitar, ba ta dauke da ranar haihuwarsa da kuma jinsi da dai sauransu, hakan ya sa ke bude wani sabon babin takaddamar da ake yi kan takardun karatun shugaba Tinubu.
Sai dai a martanin da mai taimaka wa Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai, Temitope Ajayi ya fitar a shafinsa na X (Twitter), ya ce jami’ar ta tabbatar da karatun da Tinubu ya yi a cikinta.
Hadimin shugaban, ya ce tabbatar da karutu a jami’ar da ta yi, ya nuna babu gaskiya ko kadan a zargin da ake yi cewar takardun karatun Tinubu na bogi ne.