A ci gaba da kokarin ganin ba a bar su a baya ba, wasu gungun mata a karkashin inuwar kungiyar ‘Women in Mining in Nigeria (WIMIN)’ sun kafa reshe na 27 a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja don shiga a dama da su a harkar hakar ma’adanai a fadin kasar nan.
A bikin kaddamar da shugabanin reshen na Abuja da aka yi a karshen mako, Shugabar kungiyar ta kasa, Dakta Janet Adeyemi, ta ranstar da kwamitin riko wanda Dakta Comfort Asokoro-Ogaji, za ta jagoranta kafin a kai ga zaban shugabanin kungiyar na dindindin.
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Dukkan Lambobin Zinare Na Wasannin Nutso A Gasar Wasannin Kasashen Asiya
- Barazanar Tsaro: Gwamna Kefas Ya Nemi A Tura Masa Bataliya Zuwa Taraba
A jawabinta a wajen taron, Shugabar kungiyar na kasa, Hon Adeyemi, wadda mai ilimin ma’adanai ne kuma tsohuwar ‘yar majalisar kasa ce, ta bayyana cewa, ta kafa kungiyar ce bayan da ta lura da yadda ake cutar da mata a harkar ma’adanai a Nijeriya, musamman a wuraren hakar ma’adanai na Jos da saurar sassan kasar nan, kuma ana nisantar da su daga shiga cikin harkokin kasuwancin ma’adanai a kasar nan, haka kuma ta fahimci cewa, kwararrun mata masu ilimin hakar ma’adanai na fuskantar wariya ana kuma kange su daga rike mukamai a cibiyoyi da hukumomin gudanar da harkokin ma’adanai na kasa, a kan haka ta kudiri aniyar dawo da martabar mata a harkar hakar ma’adanai a Nijeriya.
Ta kara da cewa, da farko, ta fuskanci turjiya daga maza amma ganin yadda ta dake da aiwatar da kudurinta, a halin yanzu an samu mata da dama da ke aiki a bangaren ma’adanai har an kai ga kafa reshen kungiyar a jihohi 27 cikin jihohi 36 da yankin babbar birnin tarayya, akwai kuma reshen kungiyar a kasashen Afirika da wasu sassan duniya har guda 96.
Ta kuma kara da cewa, in har mata suka hada kai a tsakaninsu, maza ba za su iya zarce su ba, musamman ganin harkar ma’adanai na da bangarori daban-daban da kowa zai iya samun nashi alharin ba tare da takurawa wai ba, tun daga masu haka, sarrfawa da saye da sayarwa da kuma fitarwa kasashen waje.
A nata jawabin, shugabar kungiyar na yankin Abuja, Dakta Comfort Asokoro-Ogaji, ta ce, za ta tabbatar da amfani da matsayinta wajen bunkasa shigar mata a harkar hakar ma’adanai a yankin Abuja.
A tattaunawar da ta yi da manema labarai, ta ce, Allah ya albarkaci yankin Abuja da ma’adanai masu muhimmanci wadanda suka hada da ‘Gold, Cassiterite, Dolomite, Lead/zinc, Marble da Tantalite’.
Ta yaba wa hukumar yankin babbar birnin Abuja a kan yadda ta kirkiro da sashin na musamman don kula da harkokin ma’adanai wanda hakan zai taimaka a gaggauta samar da aikin yi da arziki ga al’umma.
Dakta Asokoro-Ogaji ta kara da cewa, “A mastayin mu na mata za mu bayar da namu gudummawar wajen aiki a bangaren hakar ma’adanai tare da tabbatar da gwamnati na samun kudaden shiga daga bangaren hakar ma’adanai kamar yadda ya kamata.
“Ya kamata mata a yankjin Abuja su amfana da wadannan albarkatun kasa da Allah ya samar a yankin. Tabbas akwai abubuwan da suke bukatar kudi amma wasu abubuwan suna bukatar jajircewa ne kawai na al’umma, idan kowa ya bayar da nasa gudummawar dole a kai ga ci gaba wanda kuma hakan zai amfanar da al’umma gaba daya.
Bincike ya nuna cewa, mata na bayar da gaggrumin gudumawa a harkar hakar ma’adanai, amma ana amfani dasu ne kawai ba tare da suna cin cikakkiyar gajiyar aikin da suke yi ba. A kan haka aka nemi shugabannin al’umma sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su tsayu wajen ganin dukkan al’umma na cin gajiyar ma’adanai da Allah ya horewa kasa, ta hanyar amfani da kudaden da ake samu wajen gudanar da ayyuykan ci gaba ga al’umma tare da sa ido don kare muhalli daga cutarwar ayyukan masu hakar ma’adanai.