Kisan Jayland Walker, matashin Ba-Amurke dan asalin Afirka a jihar Ohio da jami’an ‘yan sanda takwas suka harba da harsashe sama da 90, ya haifar da gagarumar zanga-zanga a fadin kasar Amurka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Zhao Lijian, ya bayyana a taron manema labarai na yau da kullum Talatar nan cewa, nuna kyama da wariyar launin fata a kasar Amurka na kara ta’azzara.
Zhao Lijian ya jaddada cewa, ‘yancin dan Adam da muhimman hakkokin da daukacin bil-Adama ke morewa, ba tare da la’akari da launin fata, jinsi, yare ko addini ba, shi ne ruhin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin MDD.
A yayin da aka yi bikin ranar yaki da wariyar launin fata ta duniya ta bana, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya kira matsalar wariyar launin fata a matsayin “karfi mai duhu” da ke barazana ga kimar tsarin demokradiyya, kwanciyar hankali da zaman lafiya.
A matsayinta na kasar da ta sanya hannu kan yarjejeniyar MDD game da yaki da duk wani nau’i na wariyar launin fata, kasar Amurka ta gaza daukar managartan matakai, don magance nuna wariyar launin fata, kuma hakan keta nauyin dake bisa wuyanta ne karkashin wannan yarjejeniya.(Ibrahim)