Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin ta yi matukar bakin ciki kan yadda fararen hula suka rasa rayukansu, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Falasdinu da Isra’ila, kuma tana adawa da kuma yin tir da ayyukan da ke cutar da fararen hula.
Mao ta bayyana hakan ne yau Litinin din nan a yayin taron manema labarai na yau da kullum don yin karin haske kan rikicin dake faruwa a tsakanin Isra’ila da kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai a yankin zirin Gaza, wanda ya janyo hasarar dimbin rayuka a tsakanin bangarorin biyu.
- Xi Ya Fadawa Schumer Yadda Sin Da Amurka Za Su Daidaita Zai Tabbatar Da Makomar Bil Adama
- ‘Yan Jarida Sun Yaba Da Ci Gaba Da Al’adun Jihar Xinjiang
Mao ta ce, kasar Sin ta damu matuka game da yadda rikicin Palasdinu da Isra’ila ke ci gaba da rincabewa a baya-bayan nan, kuma ta yi matukar bakin ciki da hasarar rayukan fararen hula da rikicin ya haifar. Tana mai cewa, kasar Sin tana adawa da kuma yin tir da ayyukan da ke cutar da fararen hula.
A cewarta, kasar Sin na adawa da ayyukan da ke kara ta’azzara rikicin da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar yankin, tana kuma fatan ganin an tsagaita bude wuta da dawo da zaman lafiya nan da nan. Ta ce, ya kamata kasashen duniya su taka rawar da ta dace da kuma hada kai, don yayyafawa lamarin ruwa.
Sannan, a jiya Lahadi ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zaman gaggawa na sirri, bayan da dakarun Falasdinawa suka kaddamar da muggan hare-hare kan yankunan Isra’ila dake zirin Gaza.
Cikin tsokacin da ya yi game da hakan, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga sassan da rikicin ya shafa da su kai zuciya nesa, tare da kaucewa rura wutar rikicin.
Zhang ya kara da cewa, Sin ta yi matukar damuwa bisa dauki ba dadin da ya barke tsakanin sojojin Isra’ila da dakarun Falasdinu a Gaza, wanda hakan ya sabbaba rasuwar fararen hula masu yawa. Ya ce Sin ta damu da yiwuwar kara kazantar fadan.
Daga nan sai jami’in ya jaddada kira ga dukkanin sassan da rikicin ya shafa, da su dakile ta’azzarar fadan, su kuma amincewa matakan tsagaita bude wuta. Kaza lika su rungumi matakan ingiza kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kai ba tare da wani bata lokaci ba.
Da yammacin jiya Lahadi, kafofin watsa labaran Isra’ila da dama sun bayyana cewa, sabon fada ya kara rincabewa tsakanin sassan biyu, wanda hakan ya haifar da kisan al’ummar Isra’ila sama da 700.
A daya bangaren kuma, hukumar kiwon lafiya ta Falasdinawa dake zirin Gaza, ta fitar da sanarwa a daren jiyan, wadda a ciki ta bayyana cewa, harin sojojin Isra’ila a zirin na Gaza, ya hallaka a kalla mutane 413 tare da jikkata wasu 2300. (Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Saminu Alhassan)