A wani bangare na kokari tallafa wa yara mata kan harkar ilimi, ta cikin shirin tallafa wa karatun ‘ya’ya mata a Jihar Bauchi (AGILE) za a fara bai wa ‘yan mata a kananan makarantu da sakandire N5,000 da N10,000 don tallafa musu a harkar karatu da ba su damar zuwa makaranta a kan lokaci.
Kimanin ‘yan mata 16,260 a fadin Bauchi ne za su ci gajiyar shirin, domin cimma nasarar shirin, kowace Daliba ana so ta samu kashi 80 cikin 100 na zuwa makaranta a kowane zango.
- Kungiya Ta Nemi ‘Yan Adawa Su Rungumi Kaddara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Bauchi
- Za Mu Tabbatar An Hukunta Masu Zaluntar Kananan Yara Da Mata – Kwamishina Rabi Salisu
Ko’odinetan shirin AGILE kuma kwamishiniyar ilimi ta jihar, Dakta Jamila Muhammad Dahiru ce ta bayyana hakan ga manema labarai a karshen makon da ya gabata yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinta.
Ta ce za a rika biyan kudin ne a kowane zango domin karfafa wa dalibai guiwa su rika zuwa makaranta a ko da yaushe.
Ta kara da cewa, ana shirye-shiryen koyar da ilimin fasahar zamani don karfafawa ‘yan mata masu fasahar ilimin na’ura (ICT) damar sanya su zama masu dogaro da kansu da kuma ci gaba da neman ilimi a manyan makarantu.
Jamila ta ce, shirin na AGILE yana da burin yin abubuwa daban-daban domin tallafawa fannin ilimi ta hanyar inganta tsarin ilmantarwa a cikin yanayi mai kyau.
Ta kuma jaddada cewa, wannan shirin an yi shi ne don karfafawa ‘ya’ya mata da suka daina zuwa makaranta saboda matsalar tattalin arziki samun damar komawa makaranta su kammala matakin neman ilmin su.
AGILE – shiri ne da ya fito karkashin Bankin Duniya na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya wanda aka tsara don inganta Ilimin Sakandare ga ‘yan mata ‘yan tsakanin shekaru 10 zuwa 20.