Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo bayan ya bar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a karshen kakar wasan da ta gabata.
Hazard, mai shekara 32, ya koma Madrid ne daga Chelsea a shekarar 2019 kan kudi fam miliyan 89, amma ya buga wasanni 54 kawai a gasar La Liga.
- An Kama Masu Laifi 537, An Daure 250 Cikin Wata 3 A Borno
- Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Waje A 2024 – Kyari
Ya lashe kofunan gasar Firimiyar Ingila biyu a lokacin da yake Stamford Bridge.
“Bayan shekaru 16 da buga wasanni sama da 700, na yanke shawarar kawo karshen sana’ata a matsayin kwararren dan kwallon kafa,” in ji Hazard.
Hazard dai ya fara taka leda a kungiyar Lille ta kasar Faransa inda ya zura kwallaye 50 a wasanni 149 da ya buga sannan kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Ligue 1.
Hazard ya zura kwallaye 110 a wasanni 352 da ya buga wa Chelsea ciki har da wanda ya yi nasara a wasan karshe na gasar Europa ta 2019 da Arsenal a wasansa na karshe a kungiyar.