A yayin da ya ke karatu a jami’ar Tsinghua, dan kasar Pakistan Muhammad Wasim Asim ya taba aika wa shugaban kasar Sin Xi Jinping wata wasika tare da abokan karatu, kuma, ba da dadewa ba sun samu wasikar amsa daga wajen shugaba Xi.
Muhammad Wasim Asim ya ce, abin da ya burge shi a cikin wasikar shi ne, shugaba Xi ya ce, idan kana son zama cikin farin ciki, wajibi ne ka yi gwagwarmaya. A yayin zamansa a kasar Sin, ya ganewa idanunsa yadda aka yi gwagwarmayar kawar da kangin talauci a sassan kasar Sin. Ya ce, shirin kawar da talauci na kasar Sin ya zama abin koyi ga kasashen duniya, kuma ya baiwa kasashe masu tasowa sabbin damammakin neman ci gaba.
- Shugaba Xi Ya Yi Rangadi A Birnin Jiujiang Na Lardin Jiangxi
- Sin Ta Fitar Da Takardar Bayanai Game Da Hadin Gwiwar Ziri Daya Da Hanya Daya
Tun yana karami, Muhammad Wasim Asim ya san cewa, an saka zumunci sosai tsakanin kasashen Sin da Pakistan. Kuma, sabo da taimakon da kasar Sin ta baiwa kasarsa, da ma shawarar “Ziri daya da hanya daya”, suka sa ya samu damar yin karatu a kasar Sin.
Muhammad Wasim Asim ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping ya kan karfafa masatan kasashen duniya gwiwa, shi kuma yana son hada kan duniya baki daya. A zuciyar shugaba Xi, shi ne nauyin dake bisa wuyansa.
A ganin Muhammad Wasim Asim, irin wadannan shugabanni ba su da yawa a duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)