Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Dagacin kauyen Zazzaga Malam Usman Sarki da ke karamar hukumar Munya ta jihar Neja.
Wani jagoran al’umma a Munya da ya bukaci a saka ya sunansa ne ya bayyana wa manema labarai harin, inda ya ce, ‘yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Talata.
- Mutanen Kauye Sun Hallaka Dan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 150 A Sokoto
- Sabon Salon ‘Yan Bindiga Na Sace Daliban Jami’a Mata…
Majiyar ta ce, ‘yan bindigar sun kuma sace manoma da dama da kuma wasu mata da yara.
Kazalika majiyar ta ce, masu garkuwar sun kuma sace Shanu, Awaki da tumakai a yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kai harin amma ya ce, rundunar ba ta samu cikakken bayanai game da kai harin ba.