Filin wasa na Municipal de Portimao dake kasar Portugal na shirin karbar bakuncin wasan sada zumunci na kasa da kasa tsakanin Saudiyya da Nijeriya a ranar Juma’a, 13 ga watan Oktoba, 2023.
Nijeriya zata buga wasan ne bayan ta samu nasara akan Sao Tome & Principe da ci 6-0 a watan Satumba.
- Birmingham City Ta Nada Rooney A Matsayin Sabon Kocinta
- Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Victor Osimhen-Napol
Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen shi ne ya fi fice a cikin yan wasan Nijeriya da zasu hadu da Saudiyya.
Bayan da Super Eagles ta samu nasara a kowanne wasa ukun da ta buga na baya bayannan, za ta yi kokarin ganin ta ci gaba da taka rawar gani a karawar da zata yi da Saudiyya.
Sau daya ne Saudiyya da Nijeriya suka kara a matakin kasa da kasa a wasan sada zumunci a gabanin gasar cin kofin duniya ta 2010, inda suka tashi babu ci a filin wasa na Abuja.
A kididdigar da FIFA ta fitar, Nijeriya tana matsayi na 40 yayinda Saudiyya take matsayi na 57 a iya taka leda a Duniya.