A wani mataki na bunkasa harkokin samar da ayyukan yi ta hanyar kirkire-kirkire da fasaha, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a watan Nuwamban 2023 za ta kaddamar da zuba jarin dala miliyan 617.7 a bangaren fasahar sadarwar zamani da kirkire-kirkire ta cikin wani shiri (i-DICE) a takaice.
Domin cimma wannan nasarar, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayar da umarni ga kwamitin aiwatarwa na i-DICE da ya tabbatar ya fara gudanar da harkokin gabansa a karshen watan Nuwamban wannan shekarar.
- CMG Ya Gudanar Da Taron Bita Yayin Cika Shekara Daya Da Watsa Shirin Leaders Talk
- Sojoji Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane 6, Sun Kwato Makamai A Kaduna
A cewar wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasan, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya ce, Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar i-DICE suka ziyarceshi domin masa bayanin matakin da ake kai dangane da shirin a halin yanzu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A wajen ganawar, Shettima na nanata muhimmimancin shirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan yi a bangaren fasahar sadarwar zamani, yana mai cewa, tabbas gwamnati za ta cimma alkawuran da ta dauka a wannan fannin.
A cewarsa, ya bukaci abokan jere a shirin i-DICE da su tabbatar da sun ririta kudaden da aka ware domin tafiyar da shirin, ya ce, dala miliyan 617.7 zai kawo gagarumin sauyi muddin aka tafiyar da shi ta hanyoyin da suka dace.
“Idan aka yi nazarin kalubalen da kasar nan ke ciki da irin bukatar samar da ayyuka da matasanmu ke yi, akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen shawo kan wannan matsalar, ina rokonku da ku bayar da hadin kai domin tabbatar da shirin ya fara aiki zuwa karshen watan Nuwamba.
“Ina fatan zan ke samun bayanin aikace-aikacenku na mako-mako da zarar aka fara shirin. Kuma muna son a hanzarta gudanar da ayyukan da zai shafi dukkanin bangarorin kasar nan.”
Sai ya ba su tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya a kowani lokaci domin cimma wannan nasarar na samar da ayyuka da ceto ‘yan kasa daga halin rashin aikin yi.
Tun da farko, ministan kudi, Wale Edun, ya shaida cewar shirin zai taimaka sosai wajen cimma alkawuran da gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa ‘yan kasa na samar da ayyukan yi a bangaren kimiyyar fasahar sadarwa ga mutum miliyan 1.2.
“Tabbas dala miliyan 617 zai dauki tsawon lokaci na taimaka wa yunkurin shugaban kasa na samar da ayyukan yi da kyautata tattalin arziki musamman samar da dama ga matasa. Wani muhimman lamari a shirin shi ne kaso 50 mata ne za su amfana da wannan shirin,” ya shaida.
Shi kuma ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosus Tijjani, cewa ya yi shirin wani babban damace ga kasar nan.
“Fasaha da samar da ayyukan yi na tattalin arzikin zamani na taimakawa sosai wajen kyautata tattalin arziki. A duniyance an amince kuma an shaidi yadda fasaha ke bada damar shawo kan matsaloli da daman gaske.”
Ya kara da cewa, ta cikin shirin za a bai wa al’ummar kasa na cikin gida damar fito da fasaharsu domin taimaka wa kasar kuma su ma za su samu kudaden tafiyar da harkokin rayuwarsu.