Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da kafa wani kwamitin tsaro me mambobi 25 don kyautata sha’anin tsaro da yaki da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a fadin Jihar.
Kudirin samar na da dakarun tsaron ya biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Katsina ta dauka na samar da dakurun tsaronta da za su yi yaki da masu garkuwa da mutane da kokarin gwamnatin Jihar na dakile barazanar tsaro a jihohin yankin arewa maso yamma.
- Mutanen Kauye Sun Hallaka Dan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 150 A Sokoto
- An Horar Da ‘Ya’Yan Masu Bukata Ta Musanman Sana’o’in Hannu A Jihar Sokoto
Kwamitin wanda zai mayar da hankali kan wasu abubuwa biyar wanda Kanal Garba Moyi, da Yusha’u Ahmed Kebbe za su jagoranta a matsayin shugaba da mataimaki, sai Barista Gandi Umar Mohammed a matsayin sakataren kwamitin.
An shawarci kwamitin da ya bi hanyoyin da suka dace wajen kafa sabuwar rundunar tsaron da suka hada da kafa rundunar tsaron da daukar dakarun hukumar da samar da ingantaccen tsarin da zai kyautata sha’anin tsaro a fadin kananan hukumomin Jihar 23.
Gwamnan ya amince da kafa sabuwar rundunar tsaron ne kamar yadda yake kunshe cikin takardar da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya fitar, sai dai takardar ba ta bayyana takaimaiman lokacin da kwamitin zai mika rahoton nasa ba.