Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta karyata zargin da ake yi mata na kitsa wani shirin daukar masu laifi aiki da sunan yaki da masu aikata miyagun laifuka a jihar.
Sanarwar da Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa ya fitar, ta ce, tubabbun ’yan baranda 50 daga cikin 222 da ke haddasa tashe-tashen hankulan siyasa a jihar, amma daga baya suka mika makamansu tare da yin alkawarin ba za su koma ga tada tarzoma ba, su ne aka dauka aiki a sashe na musamman na hukumar ‘yansanda.
- Fasinjoji Sun Jikkata Yayin Da Motoci 2 Suka Yi Karo Da Juna A Legas
- Nasihar Kwankwaso Ga Angwaye Da Amaren Kano: Ku Guji Binciken Wayoyin Junanku
Shima da yake maida martani cikin gaggawa, kwamishinan ‘yansanda na jihar, Mohammad Usaini Gumel, ya caccaki sukar da aka yi wa hukumar kamar yadda ya kafe kan cewa, an horar da masu laifin bayan sun tuba kafin a tabbatar da su a matsayin ma’aikatan hukumar.
Gumel ya shaida wa manema labarai cewa, rundunar ‘yansandan ba ta yi kasa a guiwa ba wajen mayar da tsoffin ‘yan barandan siyasa zuwa sashen hukumar na musamman bisa umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce, amfani da shawarar na da matukar muhimmanci.
Ya ce, gwamnan ya yi amanna da shirin, a maimakon a bar ‘yan barandan su fada hannun miyagun ‘yan siyasa da za su iya amfani da su wajen tayar da fitina,