Ministan Harkokin Ma’adanai, Dakta Oladele Alake ya bayyana cewa, gwamnatocin jihohi basu da hurumi a dokokin Nijeriya na sanya hannu a kan yadda ake tafiyar da harkokin hakar ma’adanai a kasar nan, ya kuma ce, haramun ne yadda jihohi suke bayar da umanin dakatar da hakar ma’adanai a jihohinsu domin dokokin Nijeriya bai basu damar na yin haka ba.
Ministan ya bayyana matsayar gwamnatin tarayyar ne a taron manema labarai a Abuja a bikin ranar harkokin hakar ma’adanai na shekarar 2023.
- Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina
- Tinubu Ya Naɗa Sababbin Shugabannin Hukumomin Yaɗa Labarai
Ya ce, “Yadda jihohi ke haramta harkokin hakar ma’adanai a sassan Nijeriya abin takaici ne. Ina amfani da wannan damar na sanar da al’ummar Nijeriya cewa, babu wata jiha da take da hurumin katsalandan a harkokokin hakar ma’adanai, wanna abin da ya shafi tsarin mulkin Nijeriya ne kai tsaye.
“Hakar ma’adai abu ne da yake a matsayin hurumi na gwamnatin tarayya, kamar yadcda tsarin mulki ya zayyana. Hakki ne na gwamnatin tarayya babu tamtama a kai.
Duk wani ma’adani da Allah ya shimfida a cikin kasa mallakin gwamnatin tarayya ne, a saboda haka gwamnatin tarayya ce kadai ke da ikon tasarufin su baki daya, kamar hakar ma’adanai da lamarin albarkatun man fetur duk a karkashin gwamnatin tarayya suke. Gwamnatin taraya ce keda ikon yin dokokin da za su tafiyar da yadda za a gudanar da su a mastayin albarkar kasa mallakin al’ummar Nijeriya gaba daya.”
Ministan ya kuma ce, in har gwamnatocin jihohi na son shiga harka hakar ma’adanai sai su bi tsarin da ya dace ta hanyar karbar lasisin yin haka kamar yadda doka ta tanada.
Ya ce, gwamnatin taraya ba tana shirin fada da gwamnatocin jihohi ba ne amma za ta ci gaba da ilimantar da su a kan lamarin don a samu ci gaban da ake bukata, ya kuma ce, ya samu haduwa da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya inda suka samu fahimtar jun a a kan lamarin.
Bincike a halin yanzu ya nuna cewa, jihohin n da suka haramta hakar ma’adanai a yankin su sun hada da Kebbi, Zamfara, Taraba, da Osun.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana dalilan da ya sa suka haramta hakar ma’adanai a sassan jihar. Sakataren gwamnan jihar, Ahmed Idris, ya bayyana wa manema labarai cewa, sun haramta hakar ma’adanai a jihar ne don su daidaita yadda ake tafiyar da hakar ma’adanan a jihar.
Ya ce, “Mun yi imanin yin haka zai taimaka wa gwamnati wajen taskace kudaden shiga ta yadda za a amfana da harkar yadda ya kamata”, ya kuma ce, dakatarwa abu ne na wucin gadi.
Ita kuwa Jihar Zamfara ta bayyana cewa, ta haramta hakar ma’adanai ne saboda yadda hakar ma’adanan ya ke kara ta’azara mastalar tsaron da ake fuskanta a sassan jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Munnir Haidara ya bayyana cewa, suna sane da cewa, ba hurumin su ne haramnta hakar ma’adainai ba amma sun yi haka ne saboda a samu shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta a sassan jihar.
A watan Satumba ne Ministan hakar ma’adanai, Dele Alake, ya ba dukkan masu hakar ma’adanai ba bsia ka’ida ba da su tabbatar sun samu lasisi nan da kwanaki 30 ko kuma su fuskanci fushin hukuma, ya kuma kafa kwamitin na musamman da suka hada da ‘sojoji da ‘yansanda don samar da tsaro a wuraren hakar ma’adanai a sassan Nijeriya.