Duk da yadda ake samun rauguwar farashin kayyakin abinci a sassan duniya ciki kuwa har da kasar Amurka, Birtaniya, Yankin Turai, Afirka ta Kudu har ma da kasar Ghana, amma a Nijeriya farashin kayan abinci sai kara karuwa yake yi abin da ke nuna irin tasirin yadda janye tallafin man fetur ya haifarwa ‘yan Nijeriya da kuma yadda ya shafi darajar Naira.
Alkalumar da Hukumar Kididdaga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa, a watan Satumba na shekarar 2023 an samu hauhawar farashi har na kashi 26.72 kusan kamar yadda yake a watan Agusta 2023 inda aka samu hauhauwar farashin na kashi 25.80. hauhawar farashin da aka samu a watan Satumba ya nuna an samu karuwar kashi 0.92 na abin da aka samu a watan Agusta 2023.
- Shekaru Goma Masu Albarka: Yadda Shawarar Ziri Ɗaya Da Hanya Ɗaya Ta Yi Kyakkyawar Tasiri Ga Kasashen Afirka
- Magajin Garin Zazzau, Alh. Mansur Nuhu Bamalli Ya Rasu
Hauhawar farashin ya fi shafar kayyakin abinci inda aka samu karuwar kashi 14 (fiye da kashi 50 ke nan) daga cikin kashi 26.72 na karuwar da aka samu na farashin kayayyaki gaba daya. An kuma fi jin radadin karuwar farashin ne a manyan birane fiye da yankunan karkara saboda tsadar farashin kudin mota.
Kididdigar ya nuna cewa, a watan Satumba an samu karuwar 30.64 wanda haka abin yake a tsawon shekaru, amm kuma ya kuma karu da kashi 7.30 na abin da aka samu a watan Satumban a shekarar 2022 (kashi 23.34).
“Hauhawar farshin kayan abincin ya shafi farashin Mai, Bredi, Hatsi, Dankali, Doya, Kifi, Nama, Ganye da Madara, da kuma Kwai, kamar dai yadda kiddigar ya nuna.
A nasa tsokacin, wani Malami a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke keffi, Farfesa Uche Uwaleke ya ce, lamarin hauhawar farashin yana da tayar da hankula musamman ganin yadda darajar naira ke kara faduwa da kuma karuwar talauci a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Ya kuma dora laifin a kan yadda aka bayar da muhimmanci a kan amfani da dala a harkokin kasuwancin Nijeriya da kuma yadda ake neman kudaden kasashen waje ruwa a jallo.