Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja a daren Juma’a.
Rahotanni na cewa, wadanda iftila’in ya rutsa da su kananan yara ne, kuma lamarin ya faru ne a lokacin da injin kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji kusan 145 ya kone kurmus sakamakon wata matsala da ya samu.
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Kama Kwale-kwale Da Muggan Kwayoyin Miliyan N200 A Legas
- Dalilin Karancin Kwan Gidan Gona A Jihar Neja
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja, Ibrahim Hussain, ya ce fasinjojin sun fito ne daga kauyen da ke makwabtaka da garin Danbo na jihar Kogi.
LEADERSHIP ta rawaito cewa Jihar Neja ta sha fama da matsalolin hatsarim kwale-kwale a lokuta da dama, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji da dama a jihar.