A ranar Lahadi ne aka yi taron walima na saukar karatun Alkur’anin ‘yar jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha.
Taron walimar na Aisha Abba El-Mustapha ya gudana a gidan jarumin da ke Titin Malam Aminu Kano, kusa da Kofar Gadon Kaya, a birnin Kano.
- Jikar Dantata Ta Rasu Tana Da Shekaru 40 A Duniya
- Nijeriya Ta Yi Nasara A Kotun Ingila Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID
‘Yan uwa da abokan arziki da dama ne suka halarci walimar.
An yi karatun Alkur’ani tare da addu’o’i, sannan kuma aka raba kyaututtuka ga yara, wanda daga bisani ‘yar tasa ta yi gabatar da karatun Alkur’ani mai girma
Kamar yadda jaridar Fim Magazine ta ruwaito, ta ce El-Mustapha ya ce ya shirya taron ne domin ya nuna godiyarsa ga Allah da ya ba shi arzikin haihuwar ‘ya mai basira da kwazo, domin kuwa tana shekaru 14 da haihuwa ta yi saukar Alkur’ani.
“Ina godiya ga Allah da wannan arzikin da Allah ya ba ni kuma zan kasance mai alfahari da wannan baiwa har karshen rayuwata.
“Allah mun gode maka, kuma muna kara godiya a gare ka da wannan baiwa.
“Kuma ina fatan duk wadanda su ka zo wannan taro da ma wadanda ba su samu damar zuwa ba Allah ya hada mu a ladan.”
Alhaji Sheshe da Abubakar Bashir Maishadda na daga cikin ‘yan masana’antar Kannywood da suka halarci walimar.