Kamfanin Jiragen sama na Air Peace mai zaman kansa a Nijeriya, zai fara jigila kai tsaye zuwa birnin Guangzhou na Sin da Mumbai na Indiya, a wani yunkuri na fadada ayyukansa zuwa nahiyar Asiya.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Talata, ta ce jirgin wanda zai rika zuwa Sin sau daya a kowane mako, zai yi jigila ta farko ne a ranar 13 wata, inda zai tashi daga birnin Legas, cibiyar kasuwanci ta Nijeriya, zuwa birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Kana nan gaba cikin wannan wata, zai fara jigila zuwa India sau biyu a kowane mako.
Yana mai fatan kara yawan jigilar a nan gaba idan ayyukansa sun kankama.
A cewar sanarwar, wadannan sababbin wurare na kara tabbatar da kudurin kamfanin na hada ’yan Nijeriya da sauran sassan duniya da zurfafa dangantakar tattalin arziki da zamantakewa, tsakanin Nijeriya da kasashen biyu.
Ta kara da cewa, kamfanin Air Peace ya samu nasarori da dama cikin shekaru 7 da ya fara aiki, inda yanzu haka yake zuwa wurare 20 a cikin gida, sai wasu 7 a yankin yammacin Afrika, sai Dubai da ya fara zuwa a watan 2019 da Johanesburg a shekarar 2020. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)