Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dakta Adamu Fika kuma wanda shi ne Wazirin Fika, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, marigayin kafin rasuwarsa, ya shafa fama da kalubalen rashin lafiya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
- An Kwato Bindiga AK47 Guda 150 A Minna Bayan Artabu
Fika ya rasu a daren jiya Talata bayan ya dawo daga wani asibiti da ke Landan, zuwa wani asibitin da ke a jihar Kaduna.
Za a sallaci gawarsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a yau Laraba da karfe 4:00.
Fika, an haife shi a garin Fika, a jihar Yobe a 1933, ya kuma yi aikin gwamnati.
Ya rike mukamin shugaban jami’ia kuma ya rike mukamin shugaban tafiyar da jami’ar Ahmadu Bello ABU Zaria.
Kazalika, marigayin ya rike shugaban kwamitin amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewa ACF.
Ya fara karatunsa a kwalejin gwamanti ta Kaduna KGC da kuma kwalejin kimiyya da fasaha NCAST wacce a yanzu aka fi sani da jami’ar Ahmadu Bello.
Marigayin, ya rike mukamai da dama ciki har da babban sakatare a ma’aikatun gwamnatin tarayya kamar ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, kasuwanci da sadarwa.
Fika, ya kuma rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da kasar nan gaba.
Bugu da kari, Wazirin Fika an karrama shi da manyan lambobin yabo daga ciki akwai ta CFR da gwamnatin tarayya ta bashi a 1992.